Saboda cin zarafin mata, Mawaki 50 Cent na shirin bakuntar gidan yari
A farkon makon nan ne mawakin nan dan kasar Amurka da ya yi kaurin suna wajen cin zarafin mata, Curtis Jackson, wanda aka fi sani da lakanin ‘50 Cent’ ya debo ta da zafi, inda ya lakada wa tsohowar farkarsa duka. Ta dalilin haka, zai sa ya shiga gidan yari, madamar kotu ta kama shi […]

A farkon makon nan ne mawakin nan dan kasar Amurka da ya yi kaurin suna wajen cin zarafin mata, Curtis Jackson, wanda aka fi sani da lakanin ‘50 Cent’ ya debo ta da zafi, inda ya lakada wa tsohowar farkarsa duka. Ta dalilin haka, zai sa ya shiga gidan yari, madamar kotu ta kama shi da laifi.
Kamar yadda majiyarmu ta tabbatar, ‘50 Cent’ ya kai wa farkar tasa farmaki ne a gidanta, inda bayan ya doddoke ta, kuma ya yi kaca-kaca da kayan da ke muhallinta.
Mawakin, wanda kuma a bana ya cika shekara 38 a duniya, ya shahara da wakar gambara, musamman faya-fayansa da suka yi suna sun hada da ‘In Da Club.’ Haka kuma ya fito a matsayin dan wasa a fim din ‘Rich Or Die Trying.’
Da take gabatar da korafinta gaban ’yan sanda, tsohuwar farkar mawakin, ta shaida masu cewa, ita da shi sun samu sabani ne a yayin tattauna wani zance, sai ya shiga dukanta kuma ya lalata mata muhalli.
A yayin da ’yan sanda ke shirin gurfanar da shi gaban kotu a birinin Los Angeles, an samu tabbacin cewa madamar aka same shi da laifi, zai iya fuskantar daurin shekara biyar a gidan yari, tare da tarar Dala dubu 46.
Da take kara bayani, cewa ta yi, lokacin da sabanin ya faru a tsakaninsu, sai ta ruga ta kulle kanta a dakin kwananta, shi kuwa sai ya haure kofar dakin ya ci gaba da naushinta ta ko’ina. A sanadiyyar haka ta samu raunuka a jiki.
Jami’an ’yan sanda da ke binciken maganar, sun kiyasta cewa, mawakin ya lalata kayan gidan matar da suka kai kimanin dala dubu bakwai da dari daya.
Farkar ta shaida wa ’yan sanda cewa, sun yi soyayya da ‘50 Cent’ ta tsawon shekara uku, inda har suka haifi yarinya daya.
‘50 Cent’ dai ya yi kaurin suna ta fuskar takadaranci tun yana dan yaro. A wakokinsa, yakan yi ikirarin fadace-fadace da ta’addanci. An shaida cewa ya fara harkar muggan kwayoyi tun yana dan shekara 12 a duniya kuma an sha kai masa farmakin harbi sau tara a 2000.