Saboda Kyarar Buhari: ”Yan kasuwa sun yi wa Charly Boy duka a kasuwar Wuse

Wasu gungun matasa ta ’yan kasuwa a yau Talata sun fatattaki masu zanga-zangar neman Buhari ya sauka daga kan mulki wanda Charles Oputa da aka fi sani da Charly Boy yake jagoranta. Charley Boy ya yi ta jagorantar zanga-zangar neman sai Shugaba Buhari ya sauka daga kan mulki saboda jinyar da yake yi a kasar […]

Saboda Kyarar Buhari: ”Yan kasuwa sun yi wa Charly Boy duka a kasuwar Wuse

Wasu gungun matasa ta ’yan kasuwa a yau Talata sun fatattaki masu zanga-zangar neman Buhari ya sauka daga kan mulki wanda Charles Oputa da aka fi sani da Charly Boy yake jagoranta.
Charley Boy ya yi ta jagorantar zanga-zangar neman sai Shugaba Buhari ya sauka daga kan mulki saboda jinyar da yake yi a kasar Birtaniya.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa wadansu daga cikin ’yan kasuwar sun bayyana cewa masu zanga-zangar sun mayar da ita siyasa ba ra’ayin ’yan Najeriya suke wakilta ba.
Wani mai sayar da gwalagwalai, Malam Adamu Musa ya ce masu zanga-zangar suna da ’yancin gudanar da zanga-zangarsu amma kamata ya yi su san cewa ba shakatawa shugaban kasa ya je yi birtaniya ba.
“Ya kamata masu zanga-zangar su san cewa ba komai mutum yake sanya siyasa a ciki ba musamman batun rashin lafiya”. Inji shi
Wani Karamin Dan Kasuwa, Mista Filibus Abuh ya ce ba su yi tsammanin masu zanga-zangar za su kawo ta kasuwa ba inda talakawa ke neman abin da za su ci.
Abuh ya ce zanga-zangar ta kawo tsaiko ga harkokin kasuwar na tsawon awanni.
Mai Magana da Yawun Rundunar ’Yan Sandan Abuja, DSP Anjuguri Manzah ya fada wa Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN) cewa kawo daukin da ’yan sanda suka yi ya kawar da arangama tsakanin kungiyoyin biyu a kasuwar.
“’Yan sanda sun yi maganin matsalar kuma a yanzu su ke da iko da kasuwar”. Inji Manzah
Kamfanin Dillancin Labarai Na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa kungiyar ta gudanar da zanga-zanga a shataletalen Unity Fountain da ke tsakiyar garin Abuja.