Saboda waka makiya suka tilasta mini kwana a jeji – Nabarhama

Aminiya ta samu tattaunawa da wani mawaki mai suna Abubukar Idris, wanda ake wa lakabi da Nabarhama. Ya bayyana dalilan da suka sanya ya fara waka da nasarorin da ya samu da matsaloli da kuma kalubalen da ya fuskanta. Ga yadda hirar ta kasance: Mu fara da jin tarihinka a takaice. Sunana Abubakar Idris Nabarhama. […]

Saboda waka makiya suka tilasta mini kwana a jeji – Nabarhama
Saboda waka makiya suka tilasta mini kwana a jeji – Nabarhama

Aminiya ta samu tattaunawa da wani mawaki mai suna Abubukar Idris, wanda ake wa lakabi da Nabarhama. Ya bayyana dalilan da suka sanya ya fara waka da nasarorin da ya samu da matsaloli da kuma kalubalen da ya fuskanta. Ga yadda hirar ta kasance:

Mu fara da jin tarihinka a takaice.

Sunana Abubakar Idris Nabarhama. An haife ni a garin Nguru da ke Jihar Yobe kimanin shekaru 28 da suka gabata. Na yi makarantar allo ta tsawon shekara 13. Na yi karatu a Yobe da Maiduguri da Damaturu da garin Kiyawa da ke Jigawa kuma Zawiyyata ita ce ta Shehu Jibirila Nguru. Abin da ya sa ake kirana Nabarhama shi ne, Allah Madaukakin Rarki ne Ya sanya mini kaunar Shehu Ibrahim Inyas a zuciyata. Tun daga wannan lokaci nake sanya hotonsa a jikin kayana da agogona da wayar hannuna da abin hawana. Da mutane suka lura da haka sai suka rika kirana Abubakar Nabarhama har daga baya suke kirana Nabarhama kawai. Idan ka zo nema na idan ba ka ce Barhama ba, ba za a gane ni ba.
Me ya sa ka tsunduma cikin harkokin waka?
Dalili shi ne, tun da na taso na kasance ma’abocin karanta littattafan Hausa. Har ta kai na zama ina sha’awar rubuce-rubuce da wake-wake a harshen Hausa. Ina nan sai wani dan takara ya fito yana neman takarar kujerar gwamna a Yobe, ana kiransa Sanata Albishir. To a lokacin akwai wani mawaki a Jihar Yobe da ya yi masa waka ta zambo, ya rika muzanta shi, ni kuma a lokacin sai na ga abin da mawakin nan ya yi bai dace ba, sai na ga ya kamata na yi waka na wanke shi, don na nuna kishina ga garina da jihata. Sai na yi waka na sa mata suna ‘Gaskiyar Lamari.’ A lokacin da na yi wakar ta karbu sosai a Jihar Yobe da wasu jihohin Arewa. Tun daga wannan lokaci ne jama’a suka kara mini kwarin gwiwa na ci gaba da yin waka.
Kawo yanzu, wakoki nawa ka yi?
Na yi wakoki kamar goma, kodayake sun fi goma saboda akwai wadanda ban fito da su ba amma wadanda na san na fito da su sun kai goma. Akwai ‘Gaskiyar Lamari’ da ta ‘Sarkin Fulanin Legas’ da ta dan takarar jam’iyyar PDP na shekarar 2015 mai taken ‘Uwa Kuka ’Ya’ya Kuka’ da wacce nake ce mata ‘Mutan Yobe Ku Fito Dokta Yarima Ya Fito’ da wacce na yi a kan Azumin watan Ramadan; wacce na yi a matsayin hadaya ga mahaifina da wacce na yi wa Shehu Ibrahim Inyas da Maulana Shehi Jibrila Nguru da wacce na yi wa Manzon Allah mai taken Annabi ne ubangidanmu mu Mahammadawa da wacce na yi wa Shehi Ahmadu Tijjani da wacce na yi wa shugaban ’yan Okada da wacce na yi wa gidan wasa na Gala da sauransu.
A cikin wadannan wakoki da ka yi, wacce ka fi so?
Wakar da na fi so a cikin wakokina ita ce wacce na yi a kan Boko Haram mai suna ‘Shahada.’ Wannan waka ta Boko Haram, dalilin da ya sa na yi ta shi ne, yadda lamarin ya zama mai rikitarwa. Su ’yan Boko Haram suna ganin jihadi suke yi, su kuwa gwamnati da sauran mutanen gari suna ganin ba jihadi suke yi ba. Saboda haka sai na tsara waka na yi kira a gare su ’yan Boko Haram su auna abin da suke yi da shari’ar Allah su ga ko daidai suke yi ko ba daidai suke yi ba kuma su ji tsoron Allah su daina kashe rayukan jama’a. Na yi wannan waka ne ba don na muzanta wani ba, na yi ta ne don na ja hankalinsu da gwamnati su zauna su tattauna, a sasanta don a samu zaman lafiya a jihohinmu.
Kafin ka yi wannan waka ta Boko Haram, ba ka yi tunanin za ta iya janyo maka matsala ba?
Gaskiya na yi tunanin za ta iya janyo mani matsala, domin na san idan ba ta yi wa gwamnati dadi ba za ta iya kama ni. Haka kuma idan kuma ba ta yi wa ’yan Boko Haram dadi ba za su iya kashe ni. Shi ya sa na sa mata suna ‘Shahada.’ Kuma na san ko da an ce za a halaka ni na san na yi shahada. Shi ya sa na yi ta domin na kwato ’yancin talakawa na samar da wata kafa ta sansantawa da tattaunawa tsakanin gwamnati da ’yan Boko Haram.
Ka yi shekara nawa kana waka kuma wadanne nasarori ka samu?
Na yi shekaru biyar ina waka kuma na gode wa Allah, na samu nasarori da yawa da suka hada da gina gida da sayen mota da mallakar wadansu abubuwa na rayuwa. Ni na tashi maraya, mahaifinmu ya rasu kuma ina da kanne da suke karkashina. A cikin harkar waka na yi aure, a cikin harkar waka aka bude mini asusu a banki ana biyana albashi a Jihar Yobe.
Wane kalubale ka fuskanta?
kalubalen da na fuskanta sun hada da ganin makiya kiri-kiri da za su tare ni su zage ni, wani lokaci ma su doke ni. Akwai lokacin da sai da ta kai ba na kwana a gidana sai dai na tafi jeji na kwana saboda barazanar da ake yi mani a rayuwata.
Mene ne burinka a rayuwa?
Burin da nake so na cin mawa a waka shi ne, na samu jari, na bar yin wakar siyasa, na koma yi wa Manzon Allah waka saboda ni so nake na zama hamshakin mai begen Manzon Allah, ba mai yi wa wani waka ba.

A-Kurkura: Guba ko Magani?

Tsohon Shugaban Jami’ar Ilori, Farfesa Ambali ya rasu

ICPC ta hana El-Rufai ganin likita —Hadiminsa

Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa