Sabon albashi: Majalisar Kano ta amince da ƙarin kasafin N99bn
Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙarin kasafin kudi na N99bn domin biyan sabon mafi karancin albashi da wasu ayyukan.
Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙarin kasafin kudi na N99bn da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin biyan sabon mafi karancin albashi da wasu ayyuka.
Shugaban majalisar, Jibril Falgore, ya ce kasafin zai bai wa gwamnatin jihar damar biyan ma’aikatanta sabon mafi karancin albashin da kuma gudanar da ayyukan raya kasa.
A ranar 20 ga watan Agusta ne dai Gwamna Abba ya aikewa majalisar ƙarin kasafin na Naira biliyan 99.
Tun bayan sanya hannu kan sabuwar dokar mafi karancin albashin N70,000 jihohi da dama suka fara kafa kwamitin aiwatar da shi.
Jihar Adamawa ce ta farko wajen fara biyan mafi karancin albashin.