Sabon Firaministan Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ya kama aiki
A yammacin ranar Talatar da ta gabata ne Shugabar Jamhuriyar Tsakiyar Afirka Catherine Samba Panza ta rantsar da sabon Firaministan kasar Mahamat Kamoun.Gabannin fara aikinsa, ya bayyana irin ababan da zai fi baiwa fifiko domin a samu a cimma aiwatar da yarjejeniyar Brazzabille.Wadda za ta taimaka wajen tabbatar da tsaro da maido da martaban gwamnati […]
A yammacin ranar Talatar da ta gabata ne Shugabar Jamhuriyar Tsakiyar Afirka Catherine Samba Panza ta rantsar da sabon Firaministan kasar Mahamat Kamoun.
Gabannin fara aikinsa, ya bayyana irin ababan da zai fi baiwa fifiko domin a samu a cimma aiwatar da yarjejeniyar Brazzabille.Wadda za ta taimaka wajen tabbatar da tsaro da maido da martaban gwamnati da yi sulhu tsakanin ’yan kasar, da kuma farfado da kuma harkokin tattalin arzikin kasar.
Sai dai gabannin duka wadannan su samu, firaministan ya kammala tattaunawar da yake yi da bangarori daban-daban na kasar domin a samu kwararrun mutane, kuma ma’aikata wadanda za a nadasu a matsayin ministoci.
Kodayake, tsoffin ’yan tawayen hadaka na kungiyar Seleka sun bayyana cewa ba sa cikin wannan tafiyar.
Kyaftain Ibrahim Nedjad wani mai magana da yawun tsoffin ’yan tawayen ne, ya kuma ce: “Hakika Firaminista Mahamat Kamoun ya yi aiki karkashin tsohon Shugaba Michel Djotodia, sai dai kuma mu ba mu amince da shi ba a matsayin wani memba a hadakar Seleka ba. Sa’annan kuma game da wannan nadin ba a nemi shawarmu ba, kuma ba a nemi shawarar manyanmu ba,. Wannan hukunci gaban kanta Shugaba Panza ta yi. Saboda haka babu wani daga cikinmu da zai shiga wannan Gwamnati,” inji shi.
Sabon firaministan mai shekara 53, ya samu matsayin ne ba zato, ba tsammani, Ganin cewa baya daga cikin wadanda aka zaci cewa zai iya samun matsayin bayan murabus din tsohon Firaministan Andre Nzapayeke. Kodayake, Mista Kamoun ba bako ba ne ga jama’ar kasar saboda ya taba rike mukamin Manajan Baitul Malin a zamanin mulki hanbararren Shugaba Francois Bozize, gabannin aikinsa da gwamnatin tsohon Shugaba Michel Djotodia da kuma ta baya- bayan nan Shugaba Panza. Mista Kamoun ya fito ne daga garin Ndele da ke Arewacin kasar kuma ya yi karatunsa ne a kasar Amurka.