Sabon Firaministan Libya ya sha alwashin tabbatar da zaman lafiya a kasar

Sabon Firaministan kasar Libya Ahmed Maetig ya sha alwashin tabbatar tsaro a kasar kuma ya gargadi mayakan da ke yin gaban kansu wajen yakar masu tsananin kishin addini. Wannan na zuwa ne bayan barkewar wani sabon rikici a barke ranar Litinin, a birni na biyu mafi girma a kasar, wato Benghazi wanda ya yi sanadiyyar […]

Sabon Firaministan Libya ya sha alwashin tabbatar da zaman lafiya a kasar
Sabon Firaministan Libya ya sha alwashin tabbatar da zaman lafiya a kasar

Sabon Firaministan kasar Libya Ahmed Maetig ya sha alwashin tabbatar tsaro a kasar kuma ya gargadi mayakan da ke yin gaban kansu wajen yakar masu tsananin kishin addini.
Wannan na zuwa ne bayan barkewar wani sabon rikici a barke ranar Litinin, a birni na biyu mafi girma a kasar, wato Benghazi wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 21 da kuma jikkata wasu 82.
A watan da ya gabata ne Majalisar kasar ta zabe Mista Maetig a matsayin firaminista. A wani jawabi da ya gabatar ranar Litinin, ya ce “ a wannan lokacin da aka dora mana jagorancin kasarmu, a shirye muke da mu kare jama’a. Za mu wadata al’ummar kasar nan da tsaro kuma za mu yaki ’yan ta’adda. Ba za mu lamunci ayyukan ’yan ta’adda ba. Amma yakansu ba tare da sa hannunmu ba, ba abu ba ne da ya dace kuma zai iya jefa kasarmu cikin yakin basasa”.
Rikicin ya barke ranar Litinin tsakanin kungiyar Ansar al-Sharia da kuma mayakan da ke karbar umarnin daga tsowon Janar Khalifa Haftar. Wasu mazauna garin sun ce wannan ne mummunar tashin hankalin da suka gani tun bayan rikicin da ya barke lokacin da mayakan  da ke goyon bayan marigayi Kanar Muammar Gaddafi suka yi kokarin shigowa garin a watan Maris din shekarar 2011.
Ko a shekaranjiya Laraba, wasu mahara sun kai hari ga Janar Khalifa a gidansa na Benghazi, inda ya tsallake rijiya da baya.
kungiyar Ansar al-Sharia ta bijiro ne bayan hanbarar da Shugaba Gaddafi kuma ita ce ake wa zargin harin da aka kai karamin ofishin Jakadancin Amurka da ke Benghazi a shekarar 2012, inda Amurkawa hudu suka rasa rayukansu.