Sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas
Yanzu haka dai wasu sassan jihar sun mamaye da ruwan sama.
Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.
Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.
An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.
Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.
Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.