Sabon hari: An kashe shanu da raunata wasu a Filato
Shugaban ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) na Jihar Filato, Ibrahim Yusuf Babayo, wanda ya tabbatar da faruwar harin a ranar Juma’a a garin Jos, ya bayyana lamarin a matsayin harin ba-zata na rashin dalili.
’Yan bindiga sun kashe shanu takwas tare da jikkata wasu da dama a wani sabon hari da suka kai a ƙauyen Yarwe da ke Gundumar Fan a Ƙaramar Hukumar Barikin Ladi da ke Jihar Filato.
An kai harin ne a yammacin ranar Alhamis, Shugaban ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) na Jihar Filato, Ibrahim Yusuf Babayo, wanda ya tabbatar da faruwar harin a ranar Juma’a a garin Jos, ya bayyana lamarin a matsayin harin ba-zata na rashin dalili.
- ’Yan sanda sun kama mai yi wa ’yan bindiga safarar miyagun ƙwayoyi a Katsina
- Malama ta maka FUD a kotu, ta nemi N320m kan zargin ɓata mata suna
Babayo ya bayyana cewa, ’yan bindigar sun far wa wurin da lamarin ya faru ne sa’ilin da makiyayan ke kiwon shanunsu, ya kuma ƙara da cewa makiyayan sun tsere ne lokacin da maharan suka fara harbi ba ƙaƙautawa.
Ya ce: “Rukunin ƙungiyar MACBAN ta Jihar Filato tana la’antar kisan shanu takwas da kuma harbin wasu da dama da ake zargin maharan sa-kai na qabilar Berom ne suka yi a ƙauyen Yarwei da ke gundumar Fan a Ƙaramar Hukumar Barikin Ladi ranar Alhamis, 16 ga watan Yuli, 2026.
“Bisa rahotannin da ƙungiyar ta samu, shanu takwas ne aka kashe nan take, yayin da wasu da dama suka samu raunukan harbin bindiga a lokacin harin. Wannan lamari yana da matuƙar tayar da hankali, musamman ganin cewa yankin ya sami kwanciyar hankali na ɗan lokaci ba tare da samun irin waɗannan hare-haren ba.
“Muna fargabar cewa, wannan mummunan aiki yana da ikon lalata zaman lafiya da unguwannin Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi ke ƙoƙarin ɗorewa da shi.
Ayyukan tashin hankali ga makiyaya da hanyoyin samun hanyoyin rayuwarsu suna ƙara rura wutar rikici ne kawai, suna haifar da tsoro, kuma suna barazana ga zaman tare cikin lumana a tsakanin mutane.
“Saboda da haka, MACBAN tana kira ga Gwamnatin Jihar Filato, jami’an tsaro da duk hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta gudanar da bincike kan wannan lamari, su gano waɗanda ke da alhakin hakan, kuma su tabbatar an hukunta su daidai da doka.
Tabbatarda adalci yana da mahimmanci don hana ƙarin tashin hankali da kuma dawo da ƙwarin gwiwa tsakanin al’ummomin da abin ya shafa,” in ji shugaban.
Berom sun ƙaryata zargin
Ƙungiyar Matasan Berom (BYM), ƙarƙashin jagorancin Lauya Dalyop Solomon Mwantiri, ta karyata hannu a cikin kisan shanun.