Sabon harin Amurka da Najeriya ya kashe mayakan ISWAP 20 a Borno
A wata sanarwa, AFRICOM ta ce babu wani jami’in Amurka ko na Najeriya da ya samu ko da rauni ne a yayin harin.
Akalla mayakan kungiyar ISWAP 20 ne suka mutu a wani sabon hari da sojojin Amurka da na Najeriya suka kai musu a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Rundunar AFRICOM ta Amurka ta ce an kai harin ne bayan kashe wani kwamandan ISWAP mai suna Abu-Bilal al-Mainuki tare da wasu mayaƙansa a baya-bayan nan.
A wata sanarwa, AFRICOM ta ce babu wani jami’in Amurka ko na Najeriya da ya samu ko da rauni ne a yayin harin.
Hedikwatar Tsaro ta Najeriya kuma ta ce sama da mayaƙan ISWAP 20 ne suka mutu a harin da aka kai yankin Metele da ke Arewacin Jihar Borno.
- Kotun Abuja ta ba da belin El-Rufai a kan N100m
- Tankar mai ta faɗa cikin gida ta kashe kaka da jika a Suleja
Daraktan yaɗa labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo-Janar Samaila Uba, ya ce an kai harin ne bayan samun sahihan bayanan sirri da suka nuna taruwar mayaƙan a yankin.
Ya ce hare-haren na daga cikin karin matakan da ake ɗauka domin tarwatsa sansanonin ’yan ta’adda da hana su samun mafaka a Najeriya.
Hedikwatar Tsaron ta ta jaddada cewa dakarun Najeriya za su ci gaba da farautar duk wata ƙungiyar da ke barazana ga tsaro da zaman lafiyar Najeriya tare da tabbatar da ganin ’yan ta’adda sun kwashi kashinsu a hannu.
A karshen mako ne Shugaban Kasa Bola Tinubu tare da takwaransa na kasar Amurka, Donald Trump suka sanar cewa dakaraun hadin gwiwar kasashen biyu sun kashe Mataimakin Shugaban Kungiyar ISIS na duniya kuma jagoran kungiyar ISWAP, Abu-Bilal Al-Minuki a yankin Tafkin Chadi.