Sabon kamfanin sukari na Neja zai dauki ma’aikata dubu 10

A makon jiya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bude katafaren kamfanin sukari a garin Sunti da ke karamar Hukumar Mokwa a Jihar Neja, inda ya jinjina wa Kamfanin Fulawa na Najeriya (Nigeria Flour Mills) bisa wannan yunkuri. Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gina wannan masana’anta zai taimaka wajen inganta rayuwar al’ummar jihar musamman matasa […]

Sabon kamfanin sukari na Neja zai dauki ma’aikata dubu 10

A makon jiya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bude katafaren kamfanin sukari a garin Sunti da ke karamar Hukumar Mokwa a Jihar Neja, inda ya jinjina wa Kamfanin Fulawa na Najeriya (Nigeria Flour Mills) bisa wannan yunkuri.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gina wannan masana’anta zai taimaka wajen inganta rayuwar al’ummar jihar musamman matasa ganin yadda kasar ta fita daga koma bayan tattalin arziki, sannan ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da taimaka wa masu kokarin gina masana’antu a kasar nan.

A yayin jawabin Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello ya ce Najeriya na bukatar mayar da hankali ga bangaren noma domin bunkasa hanyoyin kasuwanci da kudaden shiga tare da samar da wadatar abinci ga kasar nan, sannan da samar da ayyukan yi ga matasa.

Ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kawo sauye-sauye da dama wadanda suka sake mayar da kasar nan kan turbar da ta dace wajen dawo da darajar harkokin noma, bayan hawanta mulki.

Gwamnan ya yaba wa salon shugabanci na Shugaba Buhari, wanda ya bullo da tsare-tsaren da suka taimaka ga farfadowar tattalin arzikin kasa da masana’antu, sannan ya ce kafa wannan masana’anta karin nasara ce ga gwamnatin tasa.

Ya yaba wa kamfanin Sulti Golden Sugars Estate da suka amince su kafa wannan masana’anta a jihar. Ya bayyana kwarin gwiwarsa na ganin kamfanin ya samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arziki ba kawai a Jihar Neja ba har ma da kasa baki daya.

Babban Daraktan kamfanin na  Sulti Golden Sugars Estate, Mista Paul Gbededo, ya bayyana cewa kamfanin wanda girmansa ya kai murabba’in hekta dubu 17, kuma ya lashe kimanin Naira biliyan 50 wurin gina shi, sannan zai rika samar da tan dubu 10 na sukari a duk shekara, kuma zai dauki ma’aikata dubu 10 a aiki.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno