Sabon katin zabe: Alamun kwaliyya za ta biya kudin sabulu
A ranar Asabar din da ta gabata ce Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC ta gudanar da gwajin yin amfani da Na`urar da za ta tantance katin kada kuri`a da za ta yi amfani dan su a cikin babban zaben kasa da za ta gudanar a ranaikun 28 ga wannan watan da […]
A ranar Asabar din da ta gabata ce Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC ta gudanar da gwajin yin amfani da Na`urar da za ta tantance katin kada kuri`a da za ta yi amfani dan su a cikin babban zaben kasa da za ta gudanar a ranaikun 28 ga wannan watan da kuma 11 ga watan Afrilu, idan Allah Ya kaimu. INEC din, ta gudanar da gwajin ne a wasu mazabu 12,dake cikin jihohi 12 na kasar nan, bayan ta zabi jihohi bi-biyu daga cikin shiyoyi shidda na kasar nan. Jihohin su ne Kabbi da Kano (shiyya arewa maso yamma), Ekiti da Legas (shiyyar kudu maso yamma), Anambra da Ebonyi (shiyyar Kudu maso Gabas), Nassarawa da Neja (shiyyar Arewa ta tsakiya), Bauchi da Taraba (shiyyar Arewa maso Gabas), sai Jihohin Delta da Ribas (shiyyar Kudu maso Kudu).
Kafin Hukumar ta INEC ta gudanar da wannan gwaji a wadancan jihohi sai da ta fara nuna gwajin ga `yan Majalisun Dokoki na kasa, wadanda suka bayyana gamsuwarsu akan irin yadda na`urorin suke aiki cikin wani dan karamin lokaci, sanna suka kuma bayar da amincewa da goyon bayansu na lallai Hukumar ta INEC ta ci gaba da shirye-shiryenta wajen yin amfani da na`urori a cikin babban zaben mai zuwa.
Dagewar da Hukumar ta INEC din ta yi na cewa ba gudu, ba ja da baya a wannan karon sai ta yi amfani da irin wadannan na`urori a wannan karon, ya kawo cece-ku ce da rashin nuna amincewa daga jam`iyyar PDP mai mulki a gwamnatin tsakiya, kai har ma da ofishin shugaban kasa, bisa ga zargin Hukumar na neman ta taimaka wa jam`iiyyar adawa ta APC a cikin zabubbukan ne. Ya yin da Hukumar ta INEC da ita kanta jam`iyyar APC, suka dage akan cewa yin amfani da na`urorin za su taimaka matuka wajen rage magudin zabe da kullum ake kuka da shi a cikin harkokin gudanar da zabubbukan kasar nan, wadanda a kullum suka zama tamfar ciwon ajali, watogwammaji da yau a wannan janhuriyar.
Tunda aka fara wannan jamhuriyar a shekarar 1999, zaben farko na 1999, da ya kawo Shugaba Cif Olusegun Obasanjo akan karagar mulki, shi kadai aka dauka sahihin zabe, shi din ma a lokacin kusan `yan siyasar kasar nan sun mayar da hankali ne akan lallai ko ta halin kaka a lallaba a kori sojoji daga kan karagar mulki, bayan sun yi shekaru 16, suna mulki ba kakkautawa. Amma dukkan zabubbuka ukun da suka biyo bayansa, wato na 2003, da na 2007, da na 2011, an ta koke-koken tafka magudi iri-iri kama daga sace akwati ko cika akwatin da kuri`un karya da yin amfani da jami`an zabe ko na tsaro don yin magudin, kamar yadda yanzu ake ta terere da irin bayanan sirrin da suka bayyana akan irin yadda ake zargin wasu jiga-jigan jam`iyyar PDP a Jihar Ekiti, sun hada baki da sojojin da aka tura daba kariyar tsaro a cikin zaben gwamnan jihar da aka yi a watan Yunin bara, inda aka ce sun taimaka wa yin gagarumin magudin zabe da ya kawo Gwamnan Jihar Mista Ayodele Fayose na jam`iyyar PDP a kan karagar mulki.
Kai karewa-ma-da-karau, shi kanshi tsohon shugaban kasa marigayi Alhaji Umaru Musa `Yar`aduwa, sai da ya amince da cewa akwai magudi cikin zaben da ya kawo shi kan karagar mulki a shekarar 2007, ta yadda hakan ta sanya ya kafa Kwamitin tsohon babban Cif Jojin kasar nan Mai shari`a Mahammadu Lawai Uwais, ya yi mashi nazarin yadda za a gyara hakan, rahoton Kwamitinsa ne ya haifar aka yi gagarumin garambawul a Dokar zabe ta 2010, amma sai dai kash! Zaben 2011, shi ma bai tsira daga mummunan magudin zabe ba kamar wadanda suka rigaye shi.
Kamar yadda Hukumar ta INEC, ta sha nanatawa tare da bada tabbaci ga ’yan kasa, cewa a wannan karon za ta yi amfani da wadannan na`urorin tantance masu kada kuri`a ne da aniyar ganin ta gare, koma ta kawo karshen magudin zaben gaba daya. Aniyar samuwar hakan ta tabbata a lokacin da aka yi wancan gwaji a wasu mazabu da aka zaba a jihohi 12, da na riga na ambata.
Da farko dai babbar fargaban da `yan kasa suke yi na irin tsawon lokacin da na`urar za ta dauka ba ta tantance mai kada kuri`a ba ya kau, domin kuwa rahotanni daga duk mazabun da aka gudanar da aikin gwajin, sun tabbatar da cewa ba inda wani mai kada kuri`a ya dauki fiye da mintuna biyu na`urar ba ta tantance shi ba, kai a wasu mazabun ma, cewa aka yi cikin dakika 15 zuwa 20, na`urarar ta tantance mai kada kuri`ar.
Babbar matsalar da ta bayyana ita ce ta mutane masu kaushin hannu walau a dalilan sana`o`in da suke yi, ko mata da suka yi lalle a hannayensu, suka kuma je tantancewar, su ne mafi yawan masu kada kuri`a da na`urar ta ki tntance su. Masu kada kuri`ar da za su fuskanci irin wannan matsala a ranaikun zabe, Hukumar ta INEC, ta ba da tabbacin cewa su sha kuruminsu, su ma za su kada kuri`unsu kamar sauran mutane, don ta ce ta tanadi wani Fom da irin wadannan mutane za su cika, sannan a ba su katin kada kuri`a a ranakun zaben don su kada wa wanda ransu ya kwanta masu da shi.
Hatta tambayar da masu adawa da wannan tsarin tantancewa suka dade suna yi ta matsalar batirin na`urar ka iya daukewa cikin ana aiki, bisa ga la`akari da karancin wutar lantarki da ake fama da ita, to, ya ya za a yi? Wannan gwaji da aka gudanar ya tabbatar da cewa wannan ba matsala ba ce, don kuwa an samu rahoton da ke tabbatar da cewa anyi aikin sa’o’i hudu a cikin aikin sa’o’i biyar na tantancewar (karfe 8 na safe zuwa karfe 1 na rana), amma karfin batir din na`urar na nan akan kashi 76 cikin 100, wato ma`ana kashi 36 cikin 100, kawai aka yi amfani da shi a sa’o’i hudu.
Babbar hikimar yin amfani da wannan na`urar tantancewa, na`urar da kasashen Afirka irin su Ghana da Kenya, zuwa yanzu suka yi amfani da su a cikin zabubbukansu, shi ne tantance adadin wadanda suka kada kuri`a, kasancewar nha`urar na kidayar dukkan mutanen da aka zura katinsu cikinta daya bayan daya, ta yadda bayan an kammala kada kuri`a za a iya tantance yawan mutane da suka kada kuri`ar a kowane akwati, ba tare da wani kace-nace ba.
Koda yake hanyoyin yin magudi a cikin zaben kasar nan suna da yawan gaske, amma dai ko ba kome, irin wannan keke-da-keke zai matukar taimakawa a rage magudin zabe. Saura da me yanzu. Tunda dai samun sahihin zabe ba na Hukumar INEC ba ne kadai. `Yan siyasa da magoya bayansu, jami`an tsaro da masu kada kuri`a kowa yana da rawar da zai taka wajen ganin a wannan karon an samu sahihi kuma ingantaccen zabe da `yan kasa da na waje kowa zai ce Madallah. Allah Ya sa yin amfani da wannan na`ura ya sa a yi zabe lami lafiya, Ya kuma ba mu ikon zaben shugabanni nagari, Ya raba mu da `yan gangan da `yan ganganci.