Sabon kocin Barcelona zai gane kurensa — Xavi

Barcelona ta kori Xavi a matsayin kocinta biyo bayan wasu kalamansa.

Sabon kocin Barcelona zai gane kurensa — Xavi

Korarren kocin Barcelona Xavi Hernandez, ya ce duk wanda zai maye gurbinsa a matsayin kocin ƙungiyar zai fuskanci ƙalubale.

Xavi, ya bayyana haka ne bayan da ya jagoranci wasan ƙarshe a matsayin kocin Barcelona, wanda suka samu nasara kan Sevilla da 2-1, a ranar Lahadi a gasar LaLiga.

A baya dai yarjejeniyar da ke tsakanin Xavi da Barcelona za ta ƙare ne a 2025, to amma a watan Janairun da ya gabata, kocin ya sanar da cewa zai raba gari da ƙungiyar a ƙarshen kakar wasannin ta bana.

Barcelona dai ta kori Xavi ne, wata guda da ta lallaɓa shi ya sauya aniyarsa ta rabuwa da ita, kamar yadda ya sanar a farkon shekarar nan.

Bayanai sun ce matakin korarsa ya biyo bayan kalaman da ya yi a kan matsalolin rashin kuɗin da suka yi wa Barcelona dabaibayi, lamarin da ya fusata shugaban ƙungiyar, Joan Laporta.

Yayin tsokaci kan matakin korarsa da aka yi, Xavi ya ce a bayyana ta ke cewar an butulcewa dukkanin ƙoƙarin da ya yi wa Barcelona a tsawon shekara biyu da rabi da ya shafe yana jagorantarta.

Xavi, ya ƙara da bai wa duk wanda zai maye gurbinsa shawarar cewa sai fa ya kasance mai haƙurin gaske a Barcelona.

Barcelona ta kammala kakar wasa ta bana a matsayin ta biyu da maki 85, tazarar maki 10 tsakaninta da zakarar LaLiga Real Madrid.