Kwamishinan Kuɗin Jihar Borno ya rasu

Ya rasu ne a safiyar Litinin a gidansa da ke Maiduguri

Kwamishinan Kuɗin Jihar Borno ya rasu

Kwamishinan Kuɗi na Jihar Borno, Ahmed Ali Ahmed, ya rasu.

Ya rasu ne a safiyar Litinin a gidansa da ke Maiduguri, babban birnin jihar.

Majiyar Aminiya da ke da kusanci da mamacin ta ce, sai da aka balla kofar dakin aka fito da gawarsa.

Ta ce, “Oga ya rasu, mun ga lokacin da ya saba fitowa ya wuce, amma bai fito ba; a ƙarshe sai da aka ɓalle kofar aka tsinci gawarsa a ciki.”

Karo na biyu ke nan cikin shekara guda, da Gwamnan Borno, Babagana Umar A Zulum ya rasa kwamishinoninsa guda biyu

Karin bayani na tafe.

Wike ya ƙwace filayen jiga-jigan ’yan siyasa a Abuja

Gwamnoni sun ƙi amincewa da ƙara harajin VAT

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana