Sabon labari: dauke sandar Majalisa da rana tsaka
Mai yiwuwa mai karatu zuwa lokacin da kake karanta wannan makala ka ji cikakkun bayanai da suka fito daga bakunan Sufeto Janar na ’yan sandan kasar nan Alhaji Ibrahim Idris da kuma shugaban hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Alhaji Lawal Musa Daurada suka yi wa Majalisar Dattawa a kan yadda wasu ’yan daba su […]
Mai yiwuwa mai karatu zuwa lokacin da kake karanta wannan makala ka ji cikakkun bayanai da suka fito daga bakunan Sufeto Janar na ’yan sandan kasar nan Alhaji Ibrahim Idris da kuma shugaban hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Alhaji Lawal Musa Daurada suka yi wa Majalisar Dattawa a kan yadda wasu ’yan daba su 5, suka kutsa kai cikin harabar Majalisar Dattawan a daidai lokacin da ta ke zama a ranar Laraban makon jiya suka kuma sungume sandar girman Majalisa. Da kuma kila jin sakamakon rahoton Kwamitinta da ta kafa don ya binci ka ma ta ta`asar. Batun mai karatu ka gamsu ko ba ka gamsu ba da bayanan da za ka ji ko ka ji na kan wa ya sa ’yan dabar kuma me ye burin da yake so ya cimmawa a kan wannan mummunar ta`asa ta ta zubar da mutuncin Majalisar da ma kasar a idanun duniya, wani batu ne na daban, don masu iya magana kan ce “Fahimta fuska.”
Na san mai karatu ya dade da jin labarin irin yadda wasu ’yan daba da ba a san ko su wane ne ba da kuma ake zargin na hannun daman Sanata ObieOmo-Agege (APC daga Jihar Delta), da suka biyo bayansa a ranar Laraban makon jiya suka samu shiga zauren Majalisar inda ba tare da wata-wata ba suka sungume sandar girman Majalisar suka kuma yi awon gaba da ita, inda bayan fitarsu suka shiga wata motar alfarma suka arce da sandar. Tuni dai Sanata Omo-Agege, ya musanta tare yake da wadancan ’yan daba. Sanatan, wanda Majalisar Dattawan ta dakatar daga halartar zaman Majalisar har na tsawon kwanaki 90, bisa ga irin kalamansa na yin adawa da sauyin fasalin yin zabubbuka a cikin daftarin gyaran dokar zabe ta shekara 2018. Gyaran da ya yi zargin cewa an yi shi ne don a muzguna wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Sanata Omo-Agegeshi ne Sakataran kungiyar ’yan Majalisar Dokoki na kasa masu goyon bayan Shugaban kasa a Majalisun.
Sungume sandar tare da arcewa da ita da ‘yan daban suka yi, ’yan daban da aka tabbatar ba mai dauke da wani mugun makami, bare sanda, sun samu ’yar tirjiya kadan daga babbar Dogarin Majalisar amma ba daga jami’an tsaron Majalisar ba irin su ’yan sanda da suke dauke da makamai, kona farin kaya, bare daga su kansu ’yan Majalisar Dattawan. Kasancewar Majalisar ita ce bangare na biyu bayan na Zartaswa wajen muhimmancin mulkin dimokradiyyar da kasar nan take ciki. Hakan ne ma ta sanya mai magana da yawun Majalisar Dattawan Sanata Aliyu Sadi Abdullahi, ya bayyana a wata sanarwa ga manema labarai cewa abin da ya faru na dauke sandar tamkar cin amanar kasa ne, kuma kokari ne na kifar da wani bangare na gwamnati da karfin tuwo, kuma afkuwar hakan tamkar cin fuska ne ga kasar nan baki daya a idon duniya. Abin da ya ce ya zama wajibi a dauki dukan matakan da suka dace wajen gano wadanda suka kitsashi, da tabbatar da an hukunta su, tare da daukar matakan ganin hakan bai sake afkuwa ba nan gaba.
Tundai a yammacin wancan yinin da aka dauke sandar girman, bayan da Majalisar ta bada wa’adin awa 24, ga Sufeto Janar na ‘yan sanda da Daraktan hukumar DSS, da lallai su tabbatar sun gano sandar da ma wadanda suka sungume ta, rundunar ’yan sanda ta kasa ta bayar da shelar ta gano sandar a kusa da gadar shigowa babban birnin tarayya Abuja, amma kuma ta ce ba ta kama ko da mutum daya ba da aka zarga da dauke sandar. Hatta shi SanataOmo-Agege da ’yan sandan suka kama bayan zaman Majalisar na wannan yini sun ce sun sake shi.
Akwai dai tambaya bisa tambaya kamar yadda na fadi a sama, da musamman ‘yan kasa suke ta neman amsoshinsu, bisa ga wancan kutse da sungume sandar Majalisa da ma tsarewa da ita tun daga cikin Majalisar har zuwa tafiya da ita, kasancewar sandar ba a aljihu aka sako ta ba, sannan kuma me tarin jami’an tsaron da aka ce a lokacin sun kai maitan da hamsin da ke ciki da wajen Majalisar, ba tare da samun wata turjiyar yunkurin hana wadancan ’yan daba fita tare da arcewa da sandar. Anyi zargin wai cewa aka yi dukkan jami’ant saron da ke Majalisar su kau da kai daga abin da ’yan dabar suka aikata. A zargi jami’an tsaron kasar nan da su kau da kai akan mummunan ta’addancin da ake aikatawa a kasar nan ba wani sabon labara ba ne, bisa la’akari da irin yadda aka saba jin zargin bada irin wadannan umarni na jami’an tsaro a lokacin zabubbuka.
Wasu kuma ’yan kasa na kallon afkuwar haka bisa ga irin zaman doya da manja da aka dade ana yi tsakanin bangaren Zartaswa da shugabancin Majalisar Dokokin, musamman Majalisar Dattawan. Kasancewar ita kanta dakatarwar da aka yi wa Sanata Omo-Agege ba ta rasa nasaba da kasancewarsa bayan na hannun daman shugaban kasa, shi ne kuma Sakataran kungiyar ’yan Majalisun Dokoki masu goyan bayan shugaba Buhari. Ba kuma wani sabon labara ba ne irin yadda yanzu shugabancin Majalisar Dattawan ya dukufa wajen ganin sai ya hana ’yan Majalisar masu ra’ayin shugaba Buhari nuna goyon bayansu ga shugaban kasar, idan aka yi la’akari da irin a kwanannan Majalisar Dattawan a duk kungiyoyin kawance da ake da su a Majalisar ta rasa wadda za ta haramta sai kungiyar su Sanata Omo-Agege.
Kamar yadda na sha fadi, a makalolina da suka gabata rashin fahimta da sabani da ake samu tsakanin bangaren Zartarwada na MajalisunDokoki ko kusa ba zai taimaka wa kowane bangare ba bare kuma ’yan kasa, don haka samun hadin kan bangarorin biyu, amma ba wanda za a rika cutar da talakawa ba, gwargwadon zarafi zai taimaka matuka wajen a rika yi wa talakawan kasar nan aiki. Ga jami’an tsaron kasa kuma lallai ya zama wajibi su iya gano wadanda suka dauke sandar da wadanda suka sa su, sannan kuma su tabbatar da an hukunta su. Kamar yadda kowa ya sani rashin yin hukunci a kasar nan na daga cikin babban abin da ke kawa wa kasar koma baya. Don haka ’yan kasa muna nan muna jiran jin yadda wannan muhimmin batu zai karke.