Sabon Masallacin Fadar Zazzau ya sake ruftowa ana tsaka da aiki
Shaidun gani da ido sun bayyana wa Aminiya cewa mutane uku sun jikkata bayan ginin ya rufto kansu.
Wani ɓangare na sabon Masallacin Fadar Zazzau ya sake ruftowa ana tsaka da aikin zuba kankaren hawa na biyu a aikin sabunta masallacin da ake yi.
Shaidun gani da ido sun bayyana wa Aminiya cewa mutane uku sun jikkata bayan ginin ya rufto kansu kuma tuni aka garzaya da su asibiti tare da killace wurin da abin ya faru.
- Iran ta gargaɗi Amurka da Isra’ila kan yiwuwar faɗaɗa yaƙi
- PDP ta tabbatar da Dankwambo a matsayin ɗan takarar Sanatan Gombe Ta Arewa
Yunƙurin jin ta bakin injiniyan da ke jagorantar aikin bai yi nasara ba, domin rahotanni sun ce ya raka waɗanda suka jikkata asibiti.
A nasa ɓangaren, Kakakin Majalisar Masarautar Zazzau, Malam Abdullahi Kwarbai, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce ba zai yi ƙarin bayani ba a halin yanzu.
Ya bayyana cewa an fara aikin sabunta masallacin ne ta hannun wani kwamitin fasaha, wanda daga bisani ya miƙa aikin ga kamfanin gine-gine.
“Saboda haka, majalisar masarautar ba za ta yi ƙarin bayani kan lamarin a wannan lokaci ba,” in ji shi.

