Sabon Ooni na Ile-Ife ya karbi sandar mulki
A ranar Litinin da ta gabata ce aka yi bikin nadin sarautar sabon Ooni na Ile-Ife, a inda Gwamnan Jihar Osun, Ebgeni Ra’uf Aregbesola ya mika masa sandar mulki; da takardar shaida da hakan ya tabbatar da sabon Oonin Babatunde Adeyeye Enitan Ogunwusi mai shekara 41 a matsayin Ooni na Ife na 51.A lokacin da […]
A ranar Litinin da ta gabata ce aka yi bikin nadin sarautar sabon Ooni na Ile-Ife, a inda Gwamnan Jihar Osun, Ebgeni Ra’uf Aregbesola ya mika masa sandar mulki; da takardar shaida da hakan ya tabbatar da sabon Oonin Babatunde Adeyeye Enitan Ogunwusi mai shekara 41 a matsayin Ooni na Ife na 51.
A lokacin da Gwamnan ke mika masa sandar mulki, ya bukaci daukacin masarautun Yarabawa da su ba sabon Oonin goyon baya domin a ci gaba da samun wanzuwar hadin kai a tsakaninsu. Ya kara da cewa ya yi matukar farin ciki da Allah Ya ba shi damar rantsar da Ooni ta hanyar mika masa sandar girma, domin a cewarsa hakan ba abu ne da kan faru a kowane lokaci ba.
Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo a wajan taron, kira ya yi ga sabon Oonin da ya yi kokarin gudanar da mulkinsa bisa gaskiya da rikon amana, ya kuma jajirce domin ci gaba da samun hadin kai a tsakanin Yarabawa da ’yan Najeriya baki daya.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, wanda ya yi jawabi a madadin sarakunan kasar nan, ya ba da tabbacin goyon bayan ilahirin sarakunan ga sabon Oonin, domin ganin ya samu cikakiyyar nasara a harkokinsa na mulki.
A jawabin, sabon Oonin na Ile-Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi Ojaja II, ya sha alwashin yin jagoranci cikin tsoron Allah, inda ya ce Allah ne Ya zabo shi ba don shi ya fi kowa ba. Don haka ya nemi hadin kan daukacin jama’a domin cin ma nasara. Ya kuma yi alkawarin damawa da matasa dari bisa dari.
Sarikin Hausawan Ile-Ife, Alhaji Mahmuda Lawal Madagali ya shaida wa Aminiya cewa Oonin shi ne shugaba ga duk wani Bayarabe a duk inda yake, domin kujerar da ya hau kujerar mulki ce ta Oduduwa, wanda shi ne asalin daukacin zuriyar Yarabawa.
Bikin nadin ya samu halartar daukacin shugabannin Yarabawa na gargajiya da na siyasa, ya kuma samu halarcin manyan sarakunan Arewa ciki har da mai alfarma sarkin Musulmi da sarkin Minna.