Sabon Rikici: An Kashe Mutane 3 A Filato

Akalla mutane uku ne aka kashe, wasu suka samu rauni a wani sabon rikici a unguwar Nkienzha da ke yankin Miango a Karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato.

Sabon Rikici: An Kashe Mutane 3 A Filato

Akalla mutane uku ne aka kashe, wasu suka samu rauni a wani sabon rikici a unguwar Nkienzha da ke yankin Miango a Karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato.

Kakakirun Rundunar Soji ta Operation Safe Haven da ke aikin samar da tsaro a jihar, Kyaftin Oya James, ya ce daukin da jami’an tsaro suka kai da wuri ya sa maharan tserewa daga yankin.

Kakakin Kungiyar Cigaban Al’ummar Irigwe (IDA), Davidson Malison, ya ce mutane biyu aka kashe a ranar Lahadi bayan an kashe wani ranar Asabar.

Kungiyar na zargin makiyaya da kai harin, amma shugaban kungiyar makiyaya Gan Allah (GAFDAN), Garba Abdullahi, ya musanta zargin.

A ranar Juma’a aka yi wa wani makiyayi mai shekaru 16 yankan rago a yankin Teegbe da ke karamar hukumar ta Bassa.

Rikicin karamar hukumar dai ya ki ci ya ki cinyewa duk da kokarin da ake yi na kawo karshensa.

An ƙaddamar wa ’yan kasuwa sabon tsarin biyan haraji a Gombe

Majalisa na son ƙirƙiro sabbin jihohi 31 a Najeriya

Malamai sun fara yajin aiki a Ebonyi

Mutuwar Almajirai: Tinubu ya buƙaci a samar da matakan kare ɗalibai