Sabon rikici ya barke a Burundi

A shekaranjiya Laraba ne rahotanni suka ce an kashe akalla mutum tara a daren Talata a Bujumbura babban birnin kasar Burundi.Wadanda suka rasa rayukansu sun hada da fararen hula takwas da dan sanda guda.An dai ji karar harbe-harbe da kuma fashewar abubuwa a wurare daban-daban da ke birnin.An kashe mutane fiye da 200 tun daga […]

Sabon rikici ya barke a Burundi
Sabon rikici ya barke a Burundi

A shekaranjiya Laraba ne rahotanni suka ce an kashe akalla mutum tara a daren Talata a Bujumbura babban birnin kasar Burundi.
Wadanda suka rasa rayukansu sun hada da fararen hula takwas da dan sanda guda.
An dai ji karar harbe-harbe da kuma fashewar abubuwa a wurare daban-daban da ke birnin.
An kashe mutane fiye da 200 tun daga watan Afrilun bana bayan da Shugaba Pierre Nkurunziza ya sanar da batun tsayarwarsa takara a karo na uku.
Wani jagoran masu fafutuka a wata kungiyar kare hakkin dan-Adam a Burundi ya shaida wa manema labarai cewa takunkumin da aka sanya wa wasu jami’an gwamnati hudu da kuma tsoffin jami’an gwamnatin zai tursasawa mahukuntan kasar fara rungumar batun sasantawa.