Sabon salo a kan rikicin makiyaya da manoma a Jihar Oyo
Wani sabon salo ya fito a kan rikicin Fulani makiyaya da manoma a Jihar Oyo, a inda suke zargin juna da yin amfani da guba da makamai da yake janyo wa kowane bangare hasara.Makiyayan sun zargi manoma da sanya gubar magani a wuraren da dabbobinsu suke shan ruwa suna mutuwa ne a yayin da manoman […]
Wani sabon salo ya fito a kan rikicin Fulani makiyaya da manoma a Jihar Oyo, a inda suke zargin juna da yin amfani da guba da makamai da yake janyo wa kowane bangare hasara.
Makiyayan sun zargi manoma da sanya gubar magani a wuraren da dabbobinsu suke shan ruwa suna mutuwa ne a yayin da manoman suke cewa, makiyaya suna tura kananan yara dauke da makamai a hannayensu da suke yi masu fyade da fashi da makami da lalata amfanin gonakinsu.
Mutane biyu masu suna Malam Sarki Gabo da Mista John Olabode Olayemi, su ne suka yi wannan zargi a gaban Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Oyo, Mista Leye Oyebade, wanda ya yi wata ganawa ta musamman da wakilan manoma da makiyaya daga kananan hukumomi 33 na jihar, a inda ya shaida masu muhimmancin zama bisa teburi daya da kyautata zamantakewa a tsakaninsu da zai samar da zama lafiya mai dorewa a Jihar.
Cikin jawabinsa ga mahalarta taron da aka gudanar a ofishinsa da ke Ibadan, Kwamishinan ya ce: “An shirya wannan zama na musamman ne domin ganawa da juna da kowane bangare na manoma da makiyaya zai fadi albarkacin bakinsa a game da hanyar da yake ganin za a yi amfani da ita wajen samar da zama lafiya. Ku tabbatar cewa, kun yi mana muhimman bayanai ba tare da nuna son rai ba da za mu yi amfani da su wajen lalubo hanyar kawo karshen wannan matsala da ta-ki-ci-ta-ki cinyewa a tsakaninku.”
Ya ce: “Kun fi kowa sanin irin matsalolin da ku ke fuskanta a cikin dazukan da kuke zaune tare. Saboda haka muke fatan za ku gaya mana gaskiya a game da wannan muhimmin al’amari da ya shafi tsaron kasa.”
Da yake tofa albarkacin bakinsa a madadin manoma daga karamar Hukumar Oorelope, Mista John Olabode Olayemi, cewa ya yi, idan ana so a kawo karshen wannan matsala to, wajibi ne a hana Fulani shiga cikin gonaki da suke lalata kayan abinci kuma a hana su rike makamai kamar bindiga da takobi da adduna da wukake a hannayensu, a lokacin da suke yawon kiwon dabbobinsu kuma a hana kananan yara da ba su kai shekaru 18 da haihuwa ba yawon kiwon dabbobi a cikin daji kuma a dakatar da yin kiwo cikin dare.
daya daga cikin wakilan Fulani makiya daga karamar Hukumar Oyo, Malam Sarki Gabo, ya zargi manoman da zuba guba a cikin ruwan da dabbobinsu ke sha, suna mutuwa ne. Ya ce: “A baya mun yi hasarar dabbobi masu yawa a dalilin shan ruwa mai dauke da guba da manoma suke watsawa a cikin kogunan da muke amfani da su wajen shayar da dabbobi. Muna sane da muhimmancin kyautata zamantakewa a tsakaninmu da manoma da sauran jama’a, domin samun kyakkyawar rayuwa amma dole ne mu girmama juna da fita hakkin juna domin samar da zaman lafiya a Jihar Oyo da kasa baki daya. Babu wanda yake farin ciki a game da hasarar da kowane bangare yake yi dangane da wannan matsala,” inji shi. Ya jinjina wa Kwamishinan ’yan sandan a kan hanzarta daukar matakin shawo kan matsaloli tsakanin manoma da makiyaya a Jihar. Ya yi alkawarin cewa, dukkan wakilan Fulani za su koma rugagensu dauke da sakamakon zaman wannan taro ga sauran jama’arsu domin duba yiwuwar fara aiki da shi.