Sabon salo: ‘Yan mata sun zama ‘yan kunar bakin wake
A halin yanzu dai masu kai hare-haren bama-bamai sun fito da wani sabon salo inda suke amfani da ‘yan mata masu kananan shekarun da ba su wuce shekara 20 ba wajen tayar da bama-baman nasu.A cikin mako guda an samu hare-haren bama bamai akalla a wurare hudu a Kano,banda wadansu wurare kimanin uku da aka […]
A halin yanzu dai masu kai hare-haren bama-bamai sun fito da wani sabon salo inda suke amfani da ‘yan mata masu kananan shekarun da ba su wuce shekara 20 ba wajen tayar da bama-baman nasu.
A cikin mako guda an samu hare-haren bama bamai akalla a wurare hudu a Kano,banda wadansu wurare kimanin uku da aka dasa bama-baman amma aka yi nasarar lalata su kafin su tashi. Hakan kuwa ya faru ne a kwanakin farko na bukukuwan sallar Idin da ta gabata.
Tun da farko mutanen jihar sun fara ji a jikinsu, a yayin da wata sanarwa da ta fito daga masarautar Kano, ta bakin Hakimin Dala, Alhaji Aminu Ado Bayero, ta bayyana cewa an soke bikin hawan dawaki a wannan sallar Idi ta bana. Yana mai nuni da cewa hukumomin jihar da kuma na johohin Arewa ne suka yanke hukuncin cewa ba za a yi hawan sallah a wadansu garuruwa na Arewan ba. Hakan na nuna cewa an samu wadansu bayanai na sirri game da shirin hare-haren ke nan.
Da misalin karfe 10 na safiyar ranar sallah ne (Lahadi) wata matashiya da aka kiyasta shekarunta sun kai 16 ta tayar da bom din da yake jikinta a kan titin kofar Nasarawa mai zuwa babban filin idi na cikin birni, yayin da wadansu ‘yansanda masu sintiri suka nemi tsayar da ita don tuhumarta. A sakamakon hakan ne ‘yansanda biyar suka samu raunuka, ita kuma ta rasu.
Ana cikin juyayin hakan sai kuma kashegarin sallah a ranar Litinin wata matar da ita ma ake kyautata zaton matashiya ce ta nufi wajen sayar da kananzir a babban gidan mai mallakar kamfanin NNPC da ke Unguwar Hotoro, kan hanyar Maiduguri,ta tayar da bam, inda ita ma a nan take ta hallaka kanta tare da mutum 3 ta kuma raunata wadansu mutum 10. Bayanai sun bayyana cewa da farko ba ta rasu ba, amma kafarta daya ta fice, har ma tana cewa mutane su yafe mata, sai daga baya ne da jami’an tsaro suka zo wajen suka karasata ta rasu.
Bayan kimanin tsawon awanni hudu zuwa biyar, wato da misalin karfe biyu zuwa uku na rana, wata matar kuma da ake jin ‘yar shekaru 18 ce ita ma ta kai harin kunar-bakin-wake a daidai kofar yamma ta filin baje koli da ke kan titin gidan zu (Zoo), kusa da Gandun Albasa.
Kafin harin bom din ‘yan wasan fim na Hausa sun yi ta bayar da sanarwa a rediyo cewa za su yi wasanni da raye-raye na bikin sallah a filin, kamar yadda suka saba a lokaci irin wannan, mutane sukan biya kudi su shiga su yi kallo. Bayanai sun nuna cewa matar ta yi kokarin a barta ta shiga filin wasan ne tun da wuri kafin a fara wasan, amma aka hana ta shiga daga bakin kofa, daga nan kuma sai ta tayar da bom din da yake jikinta.
A sheranjiya Laraba kuma wata yarinya matashiya ta sake tayar da bam da misalin karfe 2:30 na rana, inda ta kashe kanta tare da wadansu mutum biyu, mutum bakwai kuma suka jikkata. A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar KanoMagaji Majiya, ‘yar kunar bakin waken ta kai wa daliban kwalejin kimiyya da fasaha ne hari lokacin da suka je kwalejin domin duba wuraren da aka tura su domin su yi hidimar kasa.
Bayan wadannan bama-bamai da matan suka tayar, ranar jajibiri (ana gobe sallah) kuma aka gano wata mota kirar Fijo 406 a kusa da masallacin Isiyaka Rabi’u wacce aka saka mata bama-bamai aka ajiye ta da niyyar su tashi su hallaka mutane. Haka nan san samu harin bom a wani Coci bayan da masu Cocin suka kammala bautarsu, a nan ma bom din ya hallaka kimanin mutane biyar.
Jami’an tsaro sun tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa suna bincike faruwar hakan, a yayin da mutane suka yi ta bayyana ra’ayoyinsu a game da sabon salon hare-haren da ake yin amfani da mata wajen kai harin kunar bakin wake a wuraren taruwar jama’a a birnin Kano.