Sabon Salon Karbar Kudin Fansa: Dabara ko Wauta?
Yadda wasu masu neman kudin fansa suka bukaci a tura musu kudi ta banki ya daure kan Najeriya.
‘Yan bindiga
Wani lamari da ya daure wa ‘yan Najeriya da dama kai shi ne labarin yadda wasu masu satar mutane don neman kudin fansa suka bukaci a tura musu kudi ta banki.
A wannan shirin, mun yi nazari a kan abin da hakan ke nufi da kuma yanayin barayin mutanen.