Sabon salon yaki da Arewa
A ’yan kwanakin nan ne Gwamnatin Tarayya ta bayar da sanarwar cewa za ta bude wuraren kiwo na zamani da aka sanya wa suna RUGA domin amfanin daukacin makiyayan da ke fadin kasar nan. Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za a fara gwada wannan makiyaya ce a jihohi 12 da ke fadin kasar nan wadanda […]
A ’yan kwanakin nan ne Gwamnatin Tarayya ta bayar da sanarwar cewa za ta bude wuraren kiwo na zamani da aka sanya wa suna RUGA domin amfanin daukacin makiyayan da ke fadin kasar nan.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za a fara gwada wannan makiyaya ce a jihohi 12 da ke fadin kasar nan wadanda suka nuna sha’awarsu game da shirin.
Kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta nuna, an fito da tsarin ne domin kawo karshen yawace-yawacen kiwo da makiyaya ke yi wadannda suke haifar da rikici a tsakaninsu da manoma.
Saboda haka gwamnati ta ce babu ja da baya game da wannan shirin domin wata hanya ce da za ta kawo karshen rikicin manoma da makiyaya.
Mai taimaka wa Shugaban Kasa ta fuskar Watsa Labarai, Malam Garba Shehu ya ce gwamnati za ta samar da muhimman abubuwan more rayuwa a makiyayar, kamar makarantu da asibitoci da hanyoyi da asibitocin dabbobi da kasuwanni da kamfanonin sarrafa nama da sauran abubuwan da dabbobi ke samarwa da nufin kyautata su da kara musu daraja.
Haka ya ce tsarin zai amfani duk wani mutum da ke kiwo ne ba sai Bafulatani kawai ba. Ya kara da cewa tsarin zai bunkasa kiwon dabbobi tare da kara yawa da tsabtar namansu da madararsu. Haka kuma shirin zai samar da aikin yi tare da samar da hanyoyin samun bashi da tsaro ga makiyaya da kuma kawo karshen satar dabbobin.
A halin yanzu dai jihohi 12 sun bayyana wa Ma’aikatar Gona ta Tarayya sha’awarsu ta shiga shirin, inda za su samar da filaye domin fara aiwatar da tsarin.
Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ya bayyana cewa babu dalilin cece-ku-cen da ake yi game da wannan shirin domin Shugaba Buhari bai tilasta wa kowace jiha ba, wadanda suke sha’awa ne kawai za su rungumi shirin.
Ya kara da cewa, wannan shiri ne da zai amfani kasar nan da kuma jihohin da suka rungume shi domin zai taimaka wajen tabbatar da tsaro.
Idan an lura za a ga cewa wannan shiri ne mai amfani ga kasar nan baki daya, amma saboda wadansu sun lashi takobin ganin bayan gwamnati sai suka rufe idanunsu suna ta sukar lamarin da nufin gurgunta gwamnati tunda dan Arewa ne ke jagorantarta.
Ana rabewa da Fulani makiyaya ne kawai domin a yaki yankin Arewa, shi ya sanya aka sanya Fulani a gaba ana ta bata su da abin da suka yi na laifi da wanda ba su yi ba duk sai a ce su ne suka yi, kuma duk wani yunkuri da gwamnati ta yi domin inganta rayuwarsu sai wadannan ’yan baka sun soke shi. Su suke sukar Fulani da laifin tayar da fitina amma idan gwamnati ta tashi za ta yi wani abu game inganta rayuwar Fulanin domin a samu zaman lafiya sai kuma su fito su ce ba su yarda ba.
An kafa Hukumar Samar da Ilimi ga ’ya’yan makiyaya, suka ce an yi ne domin amfanin Fulani kadai, aka ce an mayar da aikin hukumar ya shafi har masunta masu yawo a bakin ruwa da ke Kudancin kasar nan.
Hukumar Ilimin ’Ya’yan Makiyayan kuma ta nemi a ba ta lasisin bude gidan rediyo domin ilimantar ’ya’yan makiyaya, suka ce ana so ne a samar da rediyon Fulani kadai, aka yi ta cece-ku-ce a kan lamarin kamar kasar nan za ta tashi.
Yanzu kuma an fito da batun samar da wuraren kiwo na zamani da nufin inganta harkar kiwo, shi ma sun taso suna ta suka saboda suna ganin harka ce da za ta amfani al’ummar Arewacin kasar nan. Abin takaici kuma shi ne, wadannan ’yan Kudun suna samun goyon bayan wadansu ’yan yankin Arewa da su ma ba su ganin alheri ga duk wani da ya shafi yankin Arewa da Gwamnatin Tarayya za ta yi saboda tsananin adawa da gwamnati.
Ya kamata gwamnonin jihohin Arewa su rungumi wannan shiri na samar da makiyaya ta zamani domin akwai dimbin amfani tattare da shi, kada su yarda soki-burutsin da wadansu masu baki ke yi ya sanya su yi sako-sako da harkar, domin yakin sunkuru ne ake yi da yankin Arewa yadda yankin zai ci gaba da zama a baya ana yi masa dariya da gorin cewa yanki ne na ci-ma-zaune.
Duk jihar da ta nuna ba ta son shirin a kyale ta, ba lallai ba tilas. Su kuma makiyaya su daure su rungumi tsarin domin akwai matukar amfani a gare su, kada su nace wajen bin tsarin iyaye da kakanni, domin zamani yana canjawa kuma kowane zamani akwai tsarin da yake zuwa da shi. Hausawa na cewa “Kowa ya ki zamani ya ki Allah.” Ya kamata al’ummar yankin Arewa su farka su fahimci cewa akwai wadanda ba su so yankin ya ci gaba, wadanda suka himmatu wajen ganin cewa duk wani abu da zai amfani yankin sai inda karfinsu ya kare wajen wargaza shi, shi ya sanya suke amfani da salo iri-iri suna yakar yankin Arewa da nufin daidaita shi.
Marigayi Malam Aminu Kano dai yana cewa “Najeriya daya ce amma kowa ya san gidan ubansa.” Idan ’yan Kudu sun zuga mu mun kona yankinmu dariya za su yi mana ba taimaka mana za su yi ba.
Yanzu sabon salon da aka fito da shi na yakar yankin Arewa shi ne sanya Fulani a gaba yadda za a muzanta su, a bata su a idon duniya domin a samu damar hallaka su, musamman da yake Bafulatani ne yake rike da shugabancin kasar a halin yanzu, saboda haka masu adawa da shi suka sanya ’yan kabilarsa a gaba.