Sabon salon zuba lefe a firinji ya kunno kai a Kano

Kayan lefe kaya ne da ango ke kai wa wadda zai aura a wani bangare na shiye-shiryen aure

Sabon salon zuba lefe a firinji ya kunno kai a Kano

Wasu kayan lefe da aka zuba a cikin firinji

Kayan lefe kaya ne da ango ke kai wa wadda zai aura a wani bangare na shiye-shiryen aure.

Duk da cewa kayan lefe al’adar Hausawa ce, a yanzu haka ya samu karbuwa a wajen sauran kabilun Arewa. Kayayyakin da ake hadawa a lokacin lefe sun hada da atamfofi da leshi-leshi da shaddoji da kayan kwalliya da jakunkuna da takalma da mayafai da kananan kayan ciki ’yan kanti da sauransu.

Yawanci akan zuba lefe a cikin akwatuna da suka kama daga guda biyu zuwa uku har zuwa 12 ko fiye, ya danganta ga karfin mai auren ko gidan da ya fito.

Sai dai a yanzu an samu bullar wani sabon yayi na zuba kayan lefe a cikin firinji maimakon akwatuna da aka saba da su.

Zahra’u Yahaya Gwammaja wata amarya ce da ake shirin yin bikinta, wacce kuma aka kawo mata lefenta a cikin firinji, ta shaida wa Aminiya cewa, ita da kanta ta nemi angonta ya zuba mata kayan lefenta a firinji.

“Kasancewar ni marainiya ce dukkan mahaifana sun rasu. Kun san kuma yadda sha’anin aure yake a al’adarmu ta Hausawa, iyayen amarya suna kashe kudi masu yawa. Su ne ke shirya gida tun daga kan shimfidar gida da labule da kayan gado da kujeru da kayan kicin.

“A wasu wuraren ma har da kayan abinci, abin da aka fi sani da gara. To ni kuma saboda na ga nauyin da ke kan ’yan uwana sun yin yawa wanda ba lallai su samu damar saya min firinji ba, don haka na gaya wa angon nawa ya zuba min lefena a cikin firinji, domin firinjin zai fi yi min amfani a kan akwatuna. Na kula idan aka kai wa amare akwatuna sai dai su ajiye su a daki suna yin kura,” in ji ta.

Amarya Zahra’u ta kara da cewa, “Haka kuma idan kin duba a duk lokacin da kika tashi sayar da akwatunan sai ki ga an karyar da su, ma’ana ba za su yi wata darajar kirki ba, ba kamar firinjin ba, wanda za ki ci moriyarsa sannan ko sayarwa kika tashi yi, za ki samu kudinsa kai wani lokacin ma har da riba.”

A cewar amaraya Zahra’u, “Lokacin da aka kawo mutane sun yi ta zuwa gidan nan don ganin lefen. Ni a zatona mutane za su kushe, amma sai na ga sun karbi abin, wasu ma suna ta nuna cewa za su yi koyi da hakan.”

Ahmad Ali shi ne angon Zahra’u ya ce, lokacin da amaryarsa ta fara kawo masa wannan shawara da farko bai amince da ita ba, amma da ya yi dogon tunani sai ya amince “Da farko da ta fara kawo min wannan shawara gaskiya ban yi na’am da ita ba. Amma sai na ce mata ta ba ni lokaci zan yi tunani a kai. To daga baya da ta rika nuna min dalilanta, inda ta nuna min firinjin zai fi ye mata amfani don haka sai na amince,” in ji shi.

A cewar angon bai samu matsala da iyayensa wajen nuna amincewarsu a kan wannan sabuwar al’ada ba. “Lokacin da na gaya wa magabatana batun yin amfani da firiji duk da cewa ba su taba jin labari ko ganin abin ba, sai suka yi na’am da shi,” in ji shi.

Wani matashi mai suna Abba Dangayu ya ce, duk da wannan dabara ta fara samun matsugunni a tsakanin talakawa, ’yan gayu da ’yan boko ba su yarda da ita.

“A watan Yuli za a yi aurena, kuma tun kusan shekara daya da ta wuce nake tarin kudin lefe, saboda sayen akwatunan zuba lefen. Da na ga abokaina su ma a firinji za su saka nasu, sai na shawarci surukaina ko ni ma za su amince min in yi haka, amma suka kada baki suka ce a’a. Dalilin da surukata ta bayar shi ne su sun riga sun saya wa ’yarsu firinjin,” in ji shi.

“Amma kin ga su abokan nawa sun yi sa’a, surukansu sun amince, don tare muka je Sabon Gari muka sayo firinjin da bai fi Naira 90,000, kuma tunda dukkanmu mun dauki lokaci muna tara lefen, su abin da suka kashe duka bai fi Naira 200,000 ba.

“A ganina wannan abu ya samu karbuwa wurin masu karamin karfi, kuma sannu a hankali zai yadu zuwa matsakaitan masu kudi da ’yan bokon ma, lura da yadda hauhawar farashin kayayyaki da fatara suke karuwa a kasar nan.

“Kun san yadda iyayenmu suke kashe makudan kudi wajen aurar da ’ya’yansu mata, su sayi kayan daki da kayan kicin, har da firinji, kuma bayan aure su bi ta da gara. Duk waɗannan ana iya yin su da mafi ƙarancin kudin da bai gaza Naira 500,000 ba. Muna sa ran wannan shi ne mafarin rushewar sauran al’adun da suke kara wa mutane nauyi,” in ji shi.

Wata matashiya mai suna Hafsa Iliyasu Musa, amarya ce ’yar wata 3, wacce aka tsara lefenta a haka, ta shaida wa Aminiya cewa da farko ba ta ji dadin wannan tsari ba, daga baya ya zamo mata gobarar titi.

“Lokacin da shi (angon) ya gaya wa iyayena cewa zai kawo lefensa a cikin firij a maimakon akwati na yi kuka sosai saboda na san kawayena za su yi ta yi min ba’a, don haka ba zai ci kaya masu yawa ba, kamar akwatuna.

Ta ce, “Na sha bacin rai na kuma dage masa ba na goyon baya, amma a karshe babu abin da zan iya yi saboda iyayena sun amince. Na dade ina bakin ciki yana lallashina. Amma fa bayan mun yi aure na gane ashe abu ne mai kyau.

“Kin san yadda a cikin Ramadan muka fuskanci tsananin zafin da ba a saba gani ba, a lokacin ne ya yi mana amfani. Idan suka kyallo wuta muna samun kankara ko ruwan sanyi. Ba mu sha fama da tsadar kankara ba. Har dariya ya rika yi min lokacin da na gaya masa. Ita ma mahaifiyata haka ta rika tsokana ta, ta ce sai in kara gode masa domin tun farko ba su da shirin saya min firinji, nauyin da ke kansu ya yi yawa.”

Hajiya Hasina Gambo uwa ce da ta aurar da ’yarta a kan irin wannan tsari, ta ce mijin ne ya shawarci surukinsu ya kawo lefensa a haka, don shi ma ya samu sauki, shi kuma ya yi maraba da hakan.

“Abu kamar wasa lokacin da ya fada, mijina ya gaya mini cewa wani abokinsa ya gaya masa cewa dansa yana amfani da firinji ya hada lefensa a maimakon akwatu domin wannan sabon salo ne. Cikin zolaya ya tambaye ni ko surukinmu zai yi haka, nan take na yarda.

“A nawa bangaren, ina fatan wannan ne mafarin karshen wadancan tsofaffin al’adu da suke yi mana illa a bukukuwan aure na Hausawa. Domin yadda wannan zamani naku ke rungumar waɗannan al’adu mutum zai yi tunanin wahayi aka yi aka ce dole sai an yi,” in ji shi.

Turmutsutsun abinci: Najeriya na fuskantar annobar yunwa – LP

An yanke wa direba hukuncin kisa kan kashe mutum 35 a China

Lalacewar jirgin ƙasa ya sa fasinjoji sun maƙale a Delta

Jerin Manyan Dambarwan Kano a 2024