Sabon Sarkin Kuwait ya caccaki gwamnati a wurin rantsar da shi
Sheikh Meshal, ya soki bangaren zartarwa da na majalisar dokokin kasar da ctuar da kasar da kuma al’ummarta
Sheikh Meshal al-Ahmad al-Sabah, ya karbi rantsuwar fara aiki a matsayin sabon Sarkin kasar Kuwait.
A jawabinsa na karbar rantsuwa, Sheikh Meshal, ya soki bangaren zartarwa da na majalisar dokokin kasar da ctuar da kasar da kuma al’ummarta.
Sheikh Meshal ya zargi mahukutan kasar da “nada mutane a mukamai ba bisa adalci ba, kuma sabanin abin da dokar kasar a tanada.”
Ya yi wannan caccaka ne a zauren majalisar da aka rantsar da shi a safiyar Laraba.
- Matalautan Najeriya sun fi na ko’ina yawa a Afirka —MDD
- An kashe mai tsaron lafiyar alkali an sace ta
Ya kuma nuna rashin amincewarsa da afuwar gwamnatin kasar ta yi wa wasu fursunoni da ’yan adawa da kuma abin da ya kira lalacewar al’adun Kuwait.
A cewarsa, “ya zama dole mu yi karatun halin da muke ciki, musamman a bangaren tsaro da tattalin arziki da kuma yanayin rayuwarmu”.
“Yana muhimmanci mu kara waiwaye da bibiya da kuma tabbatar da gaskiya bisa tsarin dokar kasa wajen yin gyara kan yadda ake watsi da rayuwar al’ummar kasa.”
Sheikh Meshal, mai shekaru 83, ya kasance mai gudanar da kasar Kuwait na yau da kullum a zamanin mulkin dan uwansa Sheikh Nawaf, saboda rashin lafiyarsa.
Sheikh Nawaf ya rasu a ranar Asabar.