Sabon shugaban APC ya yi murabus daga mukaminsa na Sanata

Sanata Abubakar Kyari mai wakiltar Borno ta Arewa, shi ma ya sanar da ajiye nasa mukamin.

Sabon shugaban APC ya yi murabus daga mukaminsa na Sanata

Sabon Shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu

Sabon shugaban Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya Sanata Abdullahi Adamu, ya ajiye mukaminsa na Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Yamma a Majalisar Dattawan kasar.

Sanata Abubakar Kyari, dan majalisa mai wakiltar Borno ta Arewa, shi ma ya sanar da ajiye nasa mukamin.

Matakin ‘yan majalisun biyu ya biyo bayan zabarsu da aka yi kan sabbin mukaman da suka hada da shugabancin jam’iyyar APC mai mulkin na Najeriya na kasa, nauyin da a yanzu ya hau kan Abdullahi Adamu, yayin da shi kuma Abubakar Kyari ya zama mataimakin shugaban jam’iyyar ta APC na yankin Arewacin Najeriya.

’Yan majalisar sun sanar da murabus din nasu ne cikin wasu wasiku daban-daban da suka aika zuwa zauren Majalisar Dattawan, wadanda shugaban majalisar Sanata Ahmad Lawan ya karanta a wannan Talatar.

A baya dai Sanata Adamu ne ke jagorancin Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da harkokin noma da raya karkara, yayin da Sanata Kyari ke shugabantar kwamitin kula da Abuja, babban birnin tarayya.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna