Sabon Shugaban Senegal ya naɗa Ousmane Sonko firaiminista

Naɗin Ousmane Sonko na zuwa ne sa’o’i kalilan bayan kammala rantsar da Shugaba Faye ranar Talata.

Sabon Shugaban Senegal ya naɗa Ousmane Sonko firaiminista

Ousmane Sonko

Sabon Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya naɗa shugaban babbar jam’iyyar adawa, Ousmane Sonko a matsayin firaiministan ƙasar.

Babban sakataren fadar shugaban kasar, Oumar Samba Ba ne ya sanar da naɗin, ta gidan talabijin ɗin kasar.

Naɗin Ousmane Sonko na zuwa ne sa’o’i kalilan bayan kammala bikin rantsar da Shugaba Faye ranar Talata a birnin Dakar.

Ousmane Sonko dai shi ne ubangidan shugaba Faye a harkokin siyasa kuma an ɗaure su a gidan yari daf da zaɓen na watan Maris.

Amma daga bisani tsohon shugaban ƙasar Macky Sall ya yi masu afuwa, tare da wasu fursunonin siyasa.

Tun da farko dai an bayyana Sonko a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar adawa amma bayan an kama shi ne sai aka yanke masa hukuncin cewa bai cancanci tsayawa takara ba – matakin da ya haifar da zanga-zanga a faɗin ƙasar.

A jawabinsa na rantsar da shi a ranar Talata, shugaba Faye ya ce Senegal za ta zama ƙasa mai babban fata tare da ƙarfafa dimokuraɗiyya.

Aminiya ta ruwaito cewa an rantsar da Bassirou Diomaye Faye a matsayin shugaban Senegal mafi ƙarancin shekaru a ƙasar da ma nahiyyar Afirka baki ɗaya.

Shugabannin Afirka da dama ciki har da na Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, sun halarci bikin rantsar da shi a garin Diamniadio kusa da babban birnin Dakar.

Tsohon ma’aikacin hukumar tattara harajin ya zama shugaban ƙasar ta Yammacin Afirka na biyar tun bayan samun ’yancin kanta a 1960.

Faye da ya yi aiki tare da mai gidansa Ousmane Sonko, wanda aka haramta wa tsayawa takara.

A yayin jawabin nasararsa ya bayyana abubuwan da za su bai wa muhimmanci da suka haɗa da sulhu tsakanin ’yan ƙasa, sauƙaƙa tsadar rayuwa da yaƙi da cin-hanci.

Sabon zaɓaɓɓen shugaban na Senegal ya kuma yi alƙawarin dawo da ƙarfin ikon ƙasar, musamman a ɓangarorin man fetur, gas da kamun kifi.

Faye na son rabuwa da kuɗin CFA franc, wanda yake kallo a matsayin gyauron mulkin mallakar Faransa, a kuma zuba jari a ɓangaren noma da manufar samar da isasshen abinci a ƙasar.