Sabon Sufeto-Janar ya fatattaki miyagu daga Inugu

An bayyana cewa sabon Sufeto-Janar na ’yan sanda, Muhammad Abubakar Adamu ya yi matukar kokarin yaki da miyagu, a lokacin da yake rike da mukamin Kwamishinan ’yan sanda a Jihar Inugu, inda ya mayar da hankali wajen tsaftace sako da lungunan da masu aikata laifuka suke boyewa a fadin jihar. A lokacin da ya isa […]

Sabon Sufeto-Janar ya fatattaki miyagu daga Inugu
Sabon Sufeto-Janar ya fatattaki miyagu daga Inugu

An bayyana cewa sabon Sufeto-Janar na ’yan sanda, Muhammad Abubakar Adamu ya yi matukar kokarin yaki da miyagu, a lokacin da yake rike da mukamin Kwamishinan ’yan sanda a Jihar Inugu, inda ya mayar da hankali wajen tsaftace sako da lungunan da masu aikata laifuka suke boyewa a fadin jihar.

A lokacin da ya isa Inugu a matsayin Kwamishina, bai dade da dawowa daga Hukumar ’Yan Sanda ta Duniya (Interpol) ba, inda ya kasance kwararren jami’i mai binciken laifuffuka, inda zuwansa ke da wuya sai ya yi amfani da kwarewarsa da ya samo daga can, ya durfafi masu garkuwa da mutane domin amsar kudin fansa da ’yan fashi da makami da dalibai ’yan kungiyar asiri da sauran muggan masu aikata laifuka da suka dade suna barazana ga al’ummar jihar.

Wani basarake mai wukar yanka a jihar, wanda kuma aboki ne ga sabon Sufeto-Janar, Igwe Emmanuel Ugwu, Basaraken Gargajiya na Ibeagwa-Nike, da ke Karamar Hukumar Inugu ta Gabas, ya ce himmar da Adamu ya nuna a jihar ta sanya masu aikata laifi suka kaura da jiyar zuwa wasu wuraren.

Igwe Ugwu ya ce ba ya da ingantattun kalmomin da zai iya bayyana irin yadda Adamu yake aikinsa cikin kwarewa da inganci,  lokacin da yake Kwamishinan’Yan sandan Jihar Enugu. “Ya rika tunkarar masu laifi kai-tsaye, ya hana su sakat a jihar,” inji shi.

Shi kuwa Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda da ke shugabantar sashen bincike a jihar, ACP Fidelis Ogarabe, ya bayyana cewa Adamu ya gudanar da aikinsa cikin tsabta da gaskiya, yana da jajircewa sannan ga kwarewa a tsarin aikinsa, lokacin da yake Kwamishina a jihar.

“Ya kasance Kwamishina mai ban al’ajabi. Ya yi amfani da kwarewar da ya samo a Hukumar ’Yan sanda ta Duniya (Interpol) ya magance matsalar masu garkuwa da mutane domin amsar kudin fansa da ’yan fashi da makami da sauransu. Babu shakka ya yi gagarumin aiki a Jihar Enugu,” inji shi.

Da ya koma kan dandantakarsa da sauran abokan aiki kuwa, Ogarabe ya ce “Adamu a matsayinsa na Kwamishina a Jihar Enugu ya gudanar da alaka mai kyau da sauran ma’aikatan da ke karkashinsa, domin kuwa shi mutum ne mai gaskiya, mai magana daya, wanda ya san aikinsa sosai.”

Shi ma Kakakin ’Yan sandan Jihar Enugu, Ebere Amaraiza da yake bayyana fahimtarsa da sabon Sufeto-Janar Adamu Muhammad, ya ce nada shi a matsayin Shugaban ’Yan sanda wani babban al’amari ne da zai kawo sauyi mai ma’ana a aikin ’yan sanda a Najeriya. “Wannan wani juyin-juya-hali ne a aikin ’yan sanda a Najeriya, domin kuwa zai gudanar da aiki bisa kwarewa da dacewa yadda ya kamata,” inji shi.

Amaraizu, wanda shi ke Kakakin ’Yan sandan  Jihar, lokacin da Adamu ke Kwamishina, ya bayyana wasu nasarori da ya samu a lokacin. “Sufeto Janar Adamu, a lokacin da yake Kwamishina a Enugu ya gudanar da wani tsarin sintiri a jihar, inda aka rika bin maboyar masu aikata laifi a lungu da sakon jihar, wanda haka ya taimaka wajen magance aika-aikarsu. Wasu daga cikin manyan nasarorinsa a lokacin sun hada da kama mutum bakwai da aka zarga da yi wa wata mata mai wa’azin Kirista kuma aka zarge su da yin garkuwa da sama da mutum goma da suka hada da manyan mutane,”inji shi.

Ebere ya ci gaba da cewa “Mu ’yan sanda da ke Jihar Enugu, muna da tabbacin cewa sabon Sufeto Janar din zai yi amfani da kwarewarsa wajen gudanar da al’amuran ’yan sandan kasar nan zuwa ga nasara. Mu a nan Enugu muna mika cikakkiyar godiya ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya nada Muhammad Abubakar Adamu a matsayin Sufeto Janar. Muna ba shi goyon baya dari bisa dari, domin ganin ya samu nasarar yaki da batagari, don samar da ingantaccen tsaro ga al’umma da dukiyarsu a Najeriya.”

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta