Sabon taken Najeriya zai magance matsalar ta’addanci —Akpabio

Sanata Godswill Akpabio ya jaddada muhimmancin sauya taken Najeriya na ‘Nigeria we hail thee’ a matsayin mafita ga matsalar ’yan bindiga

Sabon taken Najeriya zai magance matsalar ta’addanci —Akpabio

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya jaddada muhimmancin sauya taken Najeria zuwa ‘Nigeria we hail thee’ a matsayin mafita ga matsalar ’yan bindiga.

Akpabio ya bayyana cewa da tun farko ba a canza taken Najeriya daga ‘Nigeria we hail thee’ da aka koma amfani da shi ba, da watakila yanzu kasar ba ta fama da matsalar.

Shugaban majalisar ya yi wannan furuci ne a lokacin da yake bayyana dokar mayar da taken kasar zuwa ‘Nigeria we hail thee’ daga ‘Arise O compatriots’ a matsain mai matukar muhammanci.

Akpabio ya yi wannan jawabi ne a lokacin ziyarar da ya kai cibiyar nazarin harkokin majalisa da ke Abuja a ranar Talata.

A cewarsa, dokar dawo da tsohon taken kasar da kuma na ba da rancen karatu ga dalibai na naga cikin mafiya muhimmanci da Majalisa ta 10 ke alfahari da su.

A jawabin nasa, ya ci gaba da cewa ya kamata masu cewa an koma amfani da taken da turawan mulkin mallaka suka kirkiro su sani cewa kwamiti aka kafa domin jin shawarwarin al’ummar Najeriya kafin a samar da wannan take.

“Da tun lokacin an ci gaba da amfani da taken na ‘Nigeria we hail thee’ da watakila yanzu ba mu fama da matsalar ’yan bindiga.

“Domin idan har ka dauki makwabcinka a matsayin dan uwanka, babu yadda za a yi ka kashe shi,” in ji Sanata Godswill Akpabio.

NAJERIYA A YAU: Yadda Kuɗin Crypto Zai Haɓaka Tattalin Arzikin Najeriya

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji