Sabuwar cuta ta kashe mutum 4, wasu 10 sun kwanta a asibitin Kafanchan
Bullar cutar ya tilasta rufe makarantu a garin
Mutum hudu sun mutu yayin da aka killace mutum 10 a Babban Asibitin Tunawa da Patrick Ibrahim Yakowa da ke garin Kafanchan, hedkwatar Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, sanadiyyar bullar wata bakuwar cuta.
Aminiya ta lura da yadda aka kulle makarantu a garin bayan hukumominsu sun sallami dalibai da safiyar Alhamis.
Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin ga Aminiya, babbab Sakataren Asibitin, Ezra Joshua, ya ce zuwa yanzu, sun killace mutum 10 da aka kawo musu daga ranar Laraba zuwa Alhamis wanda tuni aka dauki samfurin kwayar cutar don zuwa gwaji a Kaduna don gano ko wacce irin cuta ce.
“Hakika mun samu labarin bullar wata bakuwar cuta dake farawa da zazzabi da ciwon makogwaro da ciwon kai sannan mutuwar jiki da kasala wanda zuwa yanzu mun samu labarin mutuwar mutum hudu zuwa biyar a cikin garin Kafanchan duk da ba mu tabbatar ba saboda sun rasu ne a gidajensu ba a kawo mana su asibiti mun duba su ba,” in ji shi.
Ya ce cutar tana kama yara ne ’yan shekara daya zuwa 13, kuma tana yi musu illa nan take.
Joshua, wanda ya gargadi iyaye da su yi maza su kawo duk wani yaro da suka ga alamun wannan cutar a tare da shi zuwa asibiti su daina alakanta shi da ciwon daji ko zuwa wajen masu magungunan gargajiya.
A karshe ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kaduna bisa daukin gaggawa da ta kawo yayin bullar annobar.
Ya zuwa yanzu dai gwamnatin Jihar ta Kaduna ba ta kai ga cewa wani abu ba game da sabuwar cutar.