Sabuwar hanyar noma za ta bunkasa samar da abinci a kasa – Farfesa Bindawa

An bayyana amfani da sabuwar hanyar noma ta hanyar samar da taki na gargajiya (organic farming) a matsayin abin da zai ciyar da harkar noma gaba tare da samar da ingantaccen abinci a fadin kasar nan. Shugaban Tsangayar Ayyukan noma na Jami’ar Bayero ta Kano Farfesa Mansur Auwal Bindawa ya bayyana haka a wajen taron […]

Sabuwar hanyar noma za ta bunkasa samar da abinci a kasa – Farfesa Bindawa

An bayyana amfani da sabuwar hanyar noma ta hanyar samar da taki na gargajiya (organic farming) a matsayin abin da zai ciyar da harkar noma gaba tare da samar da ingantaccen abinci a fadin kasar nan.

Shugaban Tsangayar Ayyukan noma na Jami’ar Bayero ta Kano Farfesa Mansur Auwal Bindawa ya bayyana haka a wajen taron kara wa juna sani da cibiyar (Centre For Dry Land Agriculture) ta Jami’ar Bayero ta gudanar a makon da ya gabata.

Farfesa Bindawa ya bayyana wanann sabuwar hanya a matsayin dorarriya wacce ya ce ta kunshi gudanar da bincike na zamani da kuma na kimiyya wanda zai bunkasa samuwar taki don yin noma. 

”Wannan hanya ce ta noma dorarriya da za ta samar da ingantaccen abinci wanda zai kare jiki daga kamuwa daga cututtuka irin su kansa da cutar sukari da sauransu”

Farfesan ya yi karin haske game da hanyar da ake samun wannan taki wanda ya ce ana samunsa ne a cikin gonar kai-tsaye, ita hanyar samun abin da ya hada da kashin dabbobi da tsirrai da kuma shara da sauransu “Hanyoyin da ake samun wannan sabon irin shi ne kashin dabbobi da suka hada da shanu da tumaki da awaki da kuma kaji da sauransu. Haka kuma tsirrai da ake samu daga shukar da ka yi. Misali idan kika dauki gyada da wake ko waken soya, su wadannan abubuwa Allah Ya ba su wata baiwa ta musmaman tsirran da suke fita daga jikinsu yakan zama taki wanda yake inganta kasa wajen noma  abincin na daban”

A cewar Farfesa Bindawa makasudin fito da wanann sabuwar hanya ta samar da taki don a gujewa amfani da takin zamani wajen yin noma, domin bincike ya nuna cewa dogaro tare da yin amfani da takin zamani wajen yin shuka yana kawo illa ga kasa da kuma shi kansa amfanin gona “An gano cewa amfani da takin zamani wajen yin shuka yana da illa ga kasa da kuma mafanin gona gaba daya. Abin da yake faruwa shi ne idan ka yi amfani da takin zamani wajen shuka kana girbar amfanin gona mai yawa kuma cikin sauri, to amma kuma hakan yana sa ingancin kasar ya yi ta raguwa, har a karshe ma ta daina samar da abin da ake bukata. Haka kuma yin amfani da magungunan feshi su ma suna yin illa ga shuka, don haka ta yin amfani da wannan sabuwar hanyar akwai dabaru da ake samarwa ta yadda kwarin ma ba za su taba shuka ba, wato ta hanyar amfani koriyar hanya wato yadda ake rufe shuka”

Farfesa Bindawa ya ja hankalin manoma da su rika kokarin canza abin da suke shukawa a gonakinsu, kasancewar shuka abinci guda daya yana lalata kasar noma “Abin da ake nema a harkar noma shi ne a sami ingantacciyar kasa, babu kuma abin da yake inganta kasa sai idan manomi yana kokarin canza abin da yake nomawa. Ma’ana ya zama cewar idan wannan shekara an shuka gero, shekara mai zuwa  kuma sai a juya a shuka wake ko gyada da sauransu. To idan ana juyawa hakan yana inganta noma da kuma ita kasar kanta. Ko kuma ma mutum ya rika hada shukar gaba daya, misali idan ya yi kunya hudu na gero sai ya ratsa da wake ko gyada a kunya na gaba. Idan ana zagayawa haka sai a samu gaba dayan gonar ta inganta. Haka kuma yana kawar da cututtukan kwari da sauransu.  

Shi ma a nasa jawabin, kodinetan shirin, Farfesa Joseph Joe Atungwu ya yi kira ga mahalarta taron da su tabbatar sun yi amfani da abin da suka koya musamamn a wannan lokaci da tattalin arzikin kasar nan ya koma ga ayyukan noma.

Ya bayyana cewa abincin da aka samar ta wanann sabuwar hanyar ya fi inganci akan wanda aka samar da takin zamani. “Abincin da aka samu ta wanann hanya ya fi lafiya ga jikin dan adam tare da samun karfi, haka kuma akan iya amfani da abinci wajen yin maganin wasu cututtuka,  domin ba ya dauke da wasu sinadarai”  

Wani daga cikin mahalarta taron mai suna Aliyu Abdullahi ya bayyana cewa sun amfana da wanann taro, musamamn ta wajen karin ilimi da ya samu game da yadda manomi zai habaka takin gargajiywa wato yadda za a samu taki kai tsaye daga gona ba tare da manomi ya yi amfani da takin zamani ba.

Ya yi fatan sauran manoma za su karbi wannan hanya ganin cewa hanya ce da za a samar da abinci mai lafiya, sanann kuma a bangare daya ya kawo karbuwa a wajen masu amfani da kayyyakin. “Babu shakka ni ganau ne domin na gwada wanann hanya ta yin noma, kuma amfanin gonata ya yi kyau. Idan mutum yana mafani da wanan hanya ba sai ya nemi masu sayen kayansa ba, yana zaune za a rika biyo shi har gida” Inji shi.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu