Sabuwar PDP ta bude ofishi a Abuja
A ranar Larabar da ta gabata ne wata karamar tawaga da ta kunshi mutum biyar ta balle daga Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP, inda ta bude wani sabon ofishi a gundumar Asokoro da ke babban birnin tarayya Abuja. Fusatattun mutanen da suka balle daga jam’iyyar adawar da suka hada da Prince Obi Nwosu da Alhaji […]

A ranar Larabar da ta gabata ne wata karamar tawaga da ta kunshi mutum biyar ta balle daga Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP, inda ta bude wani sabon ofishi a gundumar Asokoro da ke babban birnin tarayya Abuja.
Fusatattun mutanen da suka balle daga jam’iyyar adawar da suka hada da Prince Obi Nwosu da Alhaji Hassan Adamu da Chief Olusola Akindele da Chief Godwin Duru da kuma Franklyne Edede sun sanar da manema labarai cewa uwar jam’iyyar ta shiga rudani ne tun ranar 9 ga watan nan ne bayan kammala babban zaben shugabanninta.
Sabanin babban ofishin PDP wanda hukumar zabe mai zaman kanta ta amince da shi da ke unguwar Wuse Zone 5, wakilinmu ya bayyana cewa ana iya hangen tutoci guda biyu ne kawai a saman sabon ginin ofishin na PDP, wanda ke dauke da alamun jam’iyya.
MistaNwosu, wanda shi ne jagoran sabuwar tawagar ta mutum biyar, ya bayyana cewa a Watan Janairun sabuwar shekarar da za a shiga ne za su sanar da mambobin babban kwamitin gudanarwa ta kasa na sabuwar jam’iyyartasu.
To amma sai dai kuma, KakakinJam’iyyar PDP naQasa, MistaKola Ologbondinyan ya fitar da wata sanarwa, inda ya nuna cewa jam’iyya tasu ba ta wata matsala don an samu wasu tsirarun mutane sun yi da’awar ballewa.
“Kuma maganar gaskiya ita ce muna farin ciki tare da jinjinawa Gwamnan Jihar Bayelsa, Seriake Dickson wajen jagorantar kwamitin sulhu da sasantawa, inda suka ziyarci dukan muhimmai da kuma nagartattun ‘ya’yan jam’iyyarmu a dukan bangarorin kasar nan.
“Don haka mu a jam’iyyance ba za mu maida martini ga wasu tsiraru ko wata ‘yar tawagar daidaikun mutane ba, wadanda suka zabi yaudarar kansu bias zama ‘yan amshin shatan wata jam’iyya a game da wani mai kama da wasan kwakwayo kuma abin da riyaba,” in jishi.
Sanarwar ta kara da cewa, a karkashinja gorancin Prince Uche Secondus, za ta ci gaba da maida hankali wajen daidaita dan sabanin da aka samu a baya, don sake maida ita akan kafafunta na asali wajen sake kwace shugabancin kasa a shekarar2019.