Sabuwar PDP ta bude sabuwar sakatariya a masaukin gwamnan Adamawa

Duk da matsin lambar da shugabanin tsohuwar PDP a karkashin jagorancin Bamanga Tukur take yi musu, wadanda suka balle suka kafa sabuwar PDP a karkashin jagorancin Abubakar Kawu Baraje sun sake bude sakatariyar jam’iyyar tasu a masaukin gwamnan Adamawa da ke gida mai lamba 2 Titin Gurara a Maitama Abuja.Sai dai sun ce sakatariyar za […]

Sabuwar PDP ta bude sabuwar sakatariya a masaukin gwamnan Adamawa

Alhaji Kawu Baraje Shugaban Sabuwar PDPDuk da matsin lambar da shugabanin tsohuwar PDP a karkashin jagorancin Bamanga Tukur take yi musu, wadanda suka balle suka kafa sabuwar PDP a karkashin jagorancin Abubakar Kawu Baraje sun sake bude sakatariyar jam’iyyar tasu a masaukin gwamnan Adamawa da ke gida mai lamba 2 Titin Gurara a Maitama Abuja.
Sai dai sun ce sakatariyar za ta kasance a wannan wurin ne na wani lokaci kafin su samu wani wuri da ya fi dacewa.
A ranar Asabar da ta gabata ne dai ‘yan sanda suka rufe sakatariyar sabuwar PDP din da ke gida mai lamba 4 Orji Riber Crescent a Maitama Abuja.
Sakataren sabuwar jam’iyyar na kasa Cif Olagunsoye Oyinlola ya ce sun mayar da sakatariyar tasu zuwa masaukin gwamnan Adamawa ne saboda ba su son yin rikici da jami’an tsaro, zaman lafiya suke so shi ya sanya suka kai kara kotu.
Ya ce jam’iyyar PDP a karkashin jagorancin Baraje ba za ta yarda a tunzura ta ta yi wani abu da zai tayar da zaune tsaye ba. ‘’Domin haka muka tafi kotu kuma bayanin da Mai shari’a Elias Chukwu ya yi game da karar da muka shigar  babu wani kudundune a cikinsa da har zai jawo cece-ku-ce da nuna karfin iko.’’
Tun ranar da ‘yan’yan PDP masu korafi suka balle suka kafa sabuwar PDP a Abuja suke ta samun goyon baya a jihohin kasar nan ciki har da jihar Kaduna, jihar da mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo ya fito, inda tsohon shugaban jam’iyyar PDP na jihar Alhaji Yaro Makama Rigachikun ya jagoranci wadansu jiga-jigan jam’yyar suka nuna goyon bayansu ga sabuwar jam’iyyar PDP din. Sai dai nan da nan shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kaduna ya fito da wata sanarwa da ke nuna cewa babu wata baraka a jam’iyyar PDP ta jihar Kaduna, su Makama Rigachikun suna kokarin tayar kura ne kawai domin sun ga ba a damawa da su.
A jihar Taraba ma sabuwar jam’iyyar ta PDP ta samu magoya baya har sun bude ofis a kan titin Hammanruwa way, kusa da ofishin kamfen na ‘yar majalisar dattawa Aisha Alhassan da ke Jalingo. Amma a ranar Talata da ta gabata ‘yan sanda da yawansu ya ki kusan 20 suka yi wa ofishin dirar mikiya da misalin karfe biyu na rana suka kori masu aikin gyare-gyaren ginin sannan suka sanya kwado suka kulle wurin. Kamar yadda wani dan sabuwar PDP din ya bayyana wa Aminiya ta waya.
Amma Kakakin jam’iyyar PDP  a jihar Taraba Napoleon Adamu ya ce ‘yan sanda sun rufe ofishin ne a sakamakon wata takarda da suka samu daga Abuja da ta umarce su da yin haka. A cewarsa, uwar jam’iyya ta bayar da irin wannan umarnin ga daukacin jihohin kasar nan cewa kada a bar sabuwar jam’iyyar PDP din ta bude ofis a ko’ina.
Sai dai kuma da Aminiya ta tuntubi kakakin ‘yan sanda na jihar Taraba ASP Joseph Kwaji game da al’amarin sai ya ce babu wani abu mai kama da haka da ya faru.
Idan za a iya tunawa dai tsohon shugaban jam’iyyar PDP na jihar Taraba Dokta Abdulmumuni ya bayyana goyon bayansa ga sabuwar jam’iyyar PDP a makon da ya gabata, har ma ya bayyana sunayen shugabannin jam’iyyar tare da bayyana kansa a matsayin shugabansu.
Mai ba shugaban kasa shawara Ahmad Gulak dai ya ce bukatun da masu korafi a jam’iyyar PDP suka gabatar ya saba wa tsarin mulkin kasa da na jam’iyyar PDP. Duk da haka ya ce ana kokarin magance matsalar domin dattawan jam’iyya sun shiga tsakani domin a sasanta.
A halin yanzu dai ‘yan majalisun tarayya guda 79 sun maka shugaban jam’iyyar PDP Bamanga Tukur a kotu suna bukatar kotun ta hana shi mayar da kujerunsu a matsayin wadanda babu kowa. Daga cikinsu akwai ‘yan majalar dattawa 22 da kuma ‘yan majalisar wakilai guda 57.