Sabuwar shekara, sabon takun soyayya
A makon nan ne muka shiga sabuwar shekarar miladiyya ta 2018. A lokacin da aka ce an fita daga wata shekara zuwa wata, babu shakka akwai bukatar a waiwaya baya, a tsinkayi abubuwan da suka faru a baya cikin tunani da nazari, domin ganin cewa an saita tafiyar gaba. A wannan fili na Dausayin kauna, […]
A makon nan ne muka shiga sabuwar shekarar miladiyya ta 2018. A lokacin da aka ce an fita daga wata shekara zuwa wata, babu shakka akwai bukatar a waiwaya baya, a tsinkayi abubuwan da suka faru a baya cikin tunani da nazari, domin ganin cewa an saita tafiyar gaba.
A wannan fili na Dausayin kauna, bisa jagorancin FDk (Filfilon Dausayin kauna) mun tattauna al’amura da dama da suka shafi soyayya tsakanin al’umma. Mun fa’idantu da shawarwari, tsokaci da tambihi kala-kala daga junanmu maza da mata. Babban abin da ya saita tunaninmu da rayuwarmu ta zumunci tsakaninmu maza da mata.
Kamar yadda wasunmu suka aiko wa FDk, sun ce sun dace da zumunci da kawance, inda har ta kai su ga auratayya, wasu kuma sun ci gajiyar juna wajen abokantaka da zumunci da ’yan uwantaka. Mun gode wa Allah bisa wannan.
A yanzu da muka shiga sabuwar shekara, ya kamata mu jajirce, mu gyara zumuntarmu, mu sake kyautata niyya da saita rayuwarmu zuwa alheri ga juna. Da yardar Allah, za mu ci gaba da gudanar da wannan fili a wannan jarida.
Ni FDk, ina taya kowa da kowa murnar shiga sabuwar shekarar miladiyya, 2018. Allah Ya sa mu dace, amin!
Sakonnin Sabuwar Shekara
FDk, Assalamu alaikum, barka da sabuwar shekara. Ina amfani da wannan damar wajan taya ma’abota wannan dandalin Murnar Sabuwar Shekara. Allah Ya ba mu alheran da ke cikinta. Haka kuma ina amfani da wannan damar domin in yi kira ga ’yan uwana samari da mu yi aure domin rage yawan ’yan mata saman tituna. Na gode.
Daga Nura Muhammad Mai Apple Gusau, 08133376020.
*
FDk, zan yi amfani da wannan dama, domin yi maka tare da sauran masu bibiyar shafin nan barka da shiga sabuwar shekarar miladiyya, 2018. Ina yi mana fatan alheri, da fatan za mu ci gaba da zumunci da juna cikin kyautatawa, amin.
Daga Sadiyya Maikaka Funtuwa, 08132977172
*
Assalamu Alaikum, jinjina da ban girma a gare ku, ma’abota wannan fada mai albarka. Ina son FDk a isar mani da sakon gaisuwa zuwa ga masoyiyata (Iman). Da fatan mun shiga sabuwar shekara ta 2018 lafiya.
Daga Misbahu M. Ma’aruf ’=Yankuzo, 07062371577
Jinjina da fatan alkhairi ga FDk da ma dukkan mabiya wannan shafi mai albarka. Na samu kiraye-kiraye da dama kuma ina godiya da shawarwarin da kuka ba ni. Allah saka da alheri. Allah Ya ba mu masu sonmu domin Allah.
Daga Abdul Abu-hafiz Jihar Yobe 08066752622
*
Soyayya gamon jini
FDk da masu bibiyar wannan dandali mai albarka, barka da wannan lokaci, da fatan kowa yana cikin ƙoshin lafiya.
Soyayya gamon jini ce kuma soyayya akwai dadi, musamman idan ka yi gamon-katar da mai sonka don Allah, ba don wani ƙyale-ƙyalen duniya ba. Haka ma soyayya ta fi maɗaci ɗaci, duk lokacin Allah Ya hada ka da wadda ba ta sonka. Hmmmm, domin kuwa za ka sha mamaki!
Ya Allah Ka sa in mun tashi aure mu sami masu sonmu dominKa.
Daga Nura Muhammad Gusau, 08133376020
Sakonni dangane da Labarin Uwargida Farida
Mun samu sakonni da yawa dangane da Labarin Uwargida Farida, inda mutane da yawa suka yaba da tsarin labarin. Wasu ma sun bukaci a mayar da shi littafi domin a samu damar karanta shi a kammale wuri guda. Bisa ga wadannan shawarwari, in Allah Ya kai mu makon gobe za mu ci gaba da labarin daga inda aka tsaya. Bayan haka, ga masu bukatar cewa a mayar da shi zuwa littafi, shi ma mun amince da haka. Don haka in sha Allah nan da lokaci za a samar da littafin, wanda zai kasance da sunan: FURE: Labarin Uwargida Farida.
***
FDk, fatan alheri gare ka da sauran ’yan uwa ma’abota wannan fili. A gaskiya labarin Kishi Kumallan Mata na Farida akwai darasi sosai a cikinsa. Yana da kyau mata idan suka samu labarin mijinsu zai kara aure, su taya shi da addu’a; ba wai su dauki zafin kishi su sa a kai ba alhali karin auren ba haramun ba ne. Su ma kuma mazan sai su yi nazari sosai wajen samar wa matarsu abokiyar zama ta kirki.
Daga Shamsu dan’iya Suleja, 08036160154
Saƙon fatan alheri gare ka FDk. A gaskiya muna jin daɗin karanta wannan shafi namu. A gaskiya muna ƙaruwa a cikin wannan shafi. Bayan haka, a gaskiya Labarin Farida shi ma a gaskiya ya burge mu, mu masu karanta wannan jarida. Bayan haka don Allah a ci gaba zuwa ƙarshen wannan labara. Bayan haka don Allah samari da ’yan mata mu hada kai, ban da yaudarar juna. A riƙe alkawarin juna kuma ina neman abokan arziki maza da mata ’yan shafin FDk domin zumunci, na gode.
Daga Nasco Bebeji-Kano, 08174793546
*
Assalamu alaikum FDk, me ya sa Labarin Farida ba ya fitowa duk kowane Mako? Daga Yakub Katsina, 08035433586
*
Malam Yakub, in sha Allah za a ci gaba da labarin, kamar yadda muka sanar a bayanin farko. A ci gaba da binmu da hakuri. Mun gode. – FDk.
*
Fatan alheri a gare ka FDk, a gaskiya Labarin Kishi Kumallon Mata wato Labarin Farida ya koyar da ni darasi da dama saboda halin da mu maza muke shiga a dalilin karin aure. Sannan mu maza, ba kowace mace kawai za mu gani mu ce muna so ba, don kawai tana da kyau. Sannan ku ma mata, ku ji tsoron Allah, ku daina hana mazajenku karin aure ko haifar masu da matsala, don kawai mun ce za mu kara aure. Shin ba a aure, ke aka aure ki? Da fatan FDk za ka kara kawo mana wani labarin mai fadakarwa kamar na Farida.
Daga Murtala A.A 07068295953