Sabuwar shekara sabuwar matsala
Allah Ya kawo mu, shekara kuma ta kawo mu. Cikin ikon Allah za a wayi garin Laraba mai zuwa cikin wata sabuwar shekarar Miladiyya, kuma bisa ga dukkan alamu ba za ta sha bam-ban ba da sauran da suka shude, ba domin babu wasu alamun da ke nuna cewa za a samu gagarumin canji a […]
Allah Ya kawo mu, shekara kuma ta kawo mu. Cikin ikon Allah za a wayi garin Laraba mai zuwa cikin wata sabuwar shekarar Miladiyya, kuma bisa ga dukkan alamu ba za ta sha bam-ban ba da sauran da suka shude, ba domin babu wasu alamun da ke nuna cewa za a samu gagarumin canji a kamun ludayin gwamnatoci a harkokin gudanar da mulki. Talakawa na nuna matukar damuwa ganin yadda kowace shekara kan zo da wata matsala, sabuwa fil, maimakon shimfida matakan kawar da wadanda suka shekara suna wahalar da bayin Allah. Tun daga farkon kafuwar gwamnatin PDP a 1999, talakawan Najeriya suka shiga wani irin mawuyacin hali na rashin wadata da kuncin rayuwa da asarar rayukan iyayensu ko na ‘yan uwansu. Wannan abin ne ke sa jama’a yawan tunawa da shekarun da suka wuce, domin kuwa wanda ya tuna bara bai ji dadin bana ba.
Hujjojinsu game da haka kuwa tamkar dutse ne ba su tunkuduwa. A wajen talaka babu abin da mulkin dimokuradiyya ya tsinana masa sai ma kara karfafa rashawa da cin hanci da rashin kwanciyar hankali da hauhawar farashi da rashin aiki yi ko wata ‘yar wadata da rikicin addinni, uwa uba kuma ga tsadar mulkin dimokuradiyyar. Jami’an hukuma, musamman na tsaron rayuka da dukiyar talakwa sun halasta haram, wasu talakwa, marasa takawa, sun haramta halas. Tun da jami’an tsaro sun buge da gyangyadi, sai miyagun mutane suka samu damar watayawa, kuma ko a gaban alkalai shari’a a kashe take a faifai, mai kudi ke kwasar garabasa. Mai kara bai tsira ba, sai an karba a wajensa, wanda ake kara idan yana da kudi, komai kwarin hujjar da za a gabatar zai tsira da zunubansa.
A kowace shekara sai rayuwar talaka ta kara tsadancewa. Sabulu bai tabuwa ga talaka, balle a yi maganar maganin warkarwa ko gwadon kare sanyi. Maganin kashe sauro da soson wanka har ma da man shafawa ba wanda talaka yake iya saye rai kwance. Duk da rashin aikin yi da ya zame ruwan dare ana batar da makudan kudi don biyan albashi da alawus din bayin talakwan da aka tura wakilci a majalisu, sa’annan tsabar kudin da ake narkarwa idan an zo rajistar masu jefa kuri’a ko kuma gudanar da zabubbuka sun fi karfin abin da wasu gwamnatocin jihohi uku za su kashe a shekara, kuma a duk shekarar da zabe ya sake zagayowa sai an sake batar da dukiyar da ta nunka wacce aka kashe tun can farko. Amma duk a banza, ba a yin zaben da zai kwantar da hankalin talaka.
Wannan ne dalilin da ya sa talakawa suka raina shugabannin da siyasa ta samar masu. Talaka na kiran shugaba mayaudari, macuci, mahandami; shi kuma shugaba na kiran talaka, kidahumi, bagidaje, santolabi don ya sayar masa da ‘yancinsa. A kullum talakawa na yi wa shugabanni kallon kitse, amma idan sun gatsa sai su ji dandanon rogo. Su ma shugabanni sun mayar da talaka wani-gaso-rogo-a-ba-ka-bawo, kuma tun da suka huda jikin talaka suka ga jini, ba su bar shi ya huta ba, kullum sai sun tsotsa. Gardin mulki ya sa shugabanni yin hannun riga da talaka, shi ma talaka ya juya masu baya. Ta yaya ke nan dangantakarsu za ta sake komowa kamar ta shekarun baya, inda ake zaman mutunci da girmamawa?
Dalili ke nan da ya sa duk shekara sai matsaloli sun yi ta saukowa kasar nan ba kakkautawa, na bana yakan dara na bara kamari. Rikice-riken da kan yi katutu a cikinta, sukan buwayi duk wani mai kokarin yayyafa masu ruwa. Take-taken rarraba kawunan jama’a bisa tafarkin bambancin addini sun hana siyasa yin armashi, sa’annan kuma daga cikin shugabannin jam’iyyar da ke mulki ba mai yi wa waninsa fatan alheri sai mugun alkaba’in da zai iya kai jam’iyyarsu kasa, sa’anan kuma sun gwanance wajen kulle-kullen hana sauran jam’iyyu tasiri bisa tafarkinsu na farraka jama’a bisa manufar kabilanci.
Wannan babbar magana ce, ganin cewa duk da gawurtar jam’iyya mai mulki babu abin da ta tsinanawa kasar illa haddasa rikice-rikice da tayar da yamutsi don ta ji dadin rarraba kawunan jama’a ta yadda za ta mike kafa ta yi ta mulki har sai Mahdi ya zo, ya ture. Ta haka ne kawai za ta iya yin galaba don ta san jama’a sun dade da dawowa daga rakiyarta, saboda babu abin alherin da take tsinana masu tun bayan darewarta karagar mulki shekaru aru-aru da suka shude.
Yanzu za a shiga shekara ta goma sha biyar ke nan cikin mulkin jam’iyyar PDP a kasar nan, amma babu wani abin da ya sauya, ba ta kuma sake zani ba, har ma a wasu jihohin da ba ita ce ke mulki ba. Babu shakka shugabannin siyasar Najeriya sun ba talakawa kunya, ba domin komai ba kuwa sai don gangancinsu na dora jam’iyyunsu bisa turbar biyan bukatunsu, musamman na biye wa Turawan Yammacin Turai da Amurka. Shi ya sa kasar ta makale cikin matsalolin da suka haddasa mata, sa’anan kuma kowace sabuwar shekara tana zuwa da sababbin wahalhalun da suka gindaya mata wadanda shugabanninta ba za su iya turzawa ba don kawar da su, tun da sun ci ladan kuturu tilas ne su yi masa aski.