Sabuwar takaddama ta sake barkewa tsakanin Hameed Ali da majalisa

A yayin wata ziyara da kwamitin Majalisar Dattawa kan harkokin Kwastam ya kai shalkwatar hukumar a ranar Litinin da ya gaba ne wata takaddama ta sake kaurewa tsakanin majalisar da shugaban kwastom din.  Takaddamar ta faru ne a yayin ziyarar ta gane wa ido game da wasu kadarori da aka ce hukumar ta killace tsawon […]

Sabuwar takaddama ta sake barkewa tsakanin Hameed Ali da majalisa

A yayin wata ziyara da kwamitin Majalisar Dattawa kan harkokin Kwastam ya kai shalkwatar hukumar a ranar Litinin da ya gaba ne wata takaddama ta sake kaurewa tsakanin majalisar da shugaban kwastom din. 

Takaddamar ta faru ne a yayin ziyarar ta gane wa ido game da wasu kadarori da aka ce hukumar ta killace tsawon lokaci har sun fara lalacewa, inda shugaban kwamitin majalisar kan barnata tattalin arziki, Sanata Dino Melaye ya yi korafin cewa, kamata ya yi Shugaban Kwastam din ya sauko kasa ya tarbi ‘Yan Majaisan, a maimakon ya jira isowar tasu a zauren taron hukumar. 

Sanata Melaye ya ce, aka saba karbar bakuncin majalisar a dukkanin sauran hukumomi irin Kwastam, Gidan yari da sauransu tsawon shekaru, don haka ya ce ya yi mamakin yadda shugaban hukumar ta Kwastam ya saba wannan sananniyar ka’idar. 

Sanata Melayen, cikin fushi, ya ci gaba da shaida wa manyan jami’an kwastom din cewa, zuwan Kwamitin tamkar Majalisar ce da kanta, sannan ya bugi teburin da ke gabansa ya fara karanta takardar jawabin nasa. Jim kadan bayan kammala bayanan nasa nasa ne Shugaban hukumar ta Kwastam ya mike, inda ya fara da bayyana cewa, su fa a hukumar Kwastam, suna da na su al’adar ta daban wacce ta sha bamban da na sauran ma’aikatu.

Yana mai cewa “Ba na bukatar saukowa kasa na tarbe ku, kamar yanda mu ma a duk lokacin da muka zo Majalisarku, ba zuwa ku ke ku tarbe mu ba. Hasalima ma kwamitin naku ne ya kamata ya zo ya same ni a ofishina, ba wai ku tsaya nan dakin taro ba. Don haka ina kara tabbatar maku, mun zo hukumar kwastam ne domin mu yi wa mutane aiki.”

“Ni na karbi wannan aikin ne domin kaunar kasata, ba tare da son rai ba, don haka ba wanda zai gaya mani yi wa kasa aiki. Akan abin da ya kawo ku, wanda ku ka kira da, ‘tattalin arzikin da ake lalatawa,” zamu ba ku dukkanin hadin kai, domin aiwatar da dukkanin gyaran da ya dace in har akwai bukatar hakan,” a cewarsa. 

Anan take dai takaddamar da zafafa, wadda ta kai ga kowa ya nu na fusatarsa sannan kuma sai ‘yan Majalisun suka bijirewa daukar hoto tare da Shugabannin hukumar ta Kwastam suka yi tafiyarsu. Wanda hakan ya kara fusata Shugaban hukumar ta Kwastam, inda shi ma ya fice daga harabar hukumar cikin fushi. Sannan kuma ya yi umarni ga motocin da ke masa rakiya da su toshe duk kafofin da ‘yan Majalisun za su fita daga harabar hukumar, domin ya hana su fita kafin shi ya fita. 

Bayan ficewar shugaban Kwastam daga harabar hukumar yana busa sarewa mai dauke da alamun cin zarafi da wulakanta wakilan majalisar, bayan an tsare su har na kimanin mintuna 15, a cikin motocinsu.