Sabuwar tsintsiya ta fi dadin shara

A ranar Talata, 21 ga watan jiya ne Shugaba Muhamadu Buihari ya nada Ibrahim Kpotum Idris a matsayin sabon Sufeto-Janar na ’yan sanda , a makwafin Solomon Arase, wanda wa’adinsa na barin aiki ya cika. Nadin Idris ya bai wa  jama’a da yawa mamaki ganin cewa akwai wasu mutane guda shida a gabansa, wadanda kuma […]

Sabuwar tsintsiya ta fi dadin shara
Sabuwar tsintsiya ta fi dadin shara

A ranar Talata, 21 ga watan jiya ne Shugaba Muhamadu Buihari ya nada Ibrahim Kpotum Idris a matsayin sabon Sufeto-Janar na ’yan sanda , a makwafin Solomon Arase, wanda wa’adinsa na barin aiki ya cika. Nadin Idris ya bai wa  jama’a da yawa mamaki ganin cewa akwai wasu mutane guda shida a gabansa, wadanda kuma suka girme shi a aikin dansanda.  Ashe ke nan ana iya cewa akwai wasu abubuwa ko halaye da suka sanya aka ga shi ne dai ya fi dacewa, domin ko ba komai an  shaide shi  da kasancewa  mutum ne wanda ba ruwansa da rashawa, bai kuma karbar cin hanci .
Sabon Sufeto-Janar na ‘Yan sandan  zai kama aiki ne a mawuyacin lokacin  da ake cewa mutuncin aikin dansanda ya kusan zubewa kasa warwas, sa’anan kuma su ‘yan sandan ba su da wata kima a idanun jama’a.  A wajen talakan Najeriya matsayin dansanda dai bai wuce azzalumi, maketaci, mai son kansa da kuma kaunar haram fiye da neman halaliya ba, sa’annan kuma uwa-uba ga tsananin rashin gaskiya da saurin cin amana. Dangane da haka ne dukkan masoyansa ke tausaya masa domin halin da yake ciki, babu kuma wanda zai yi masa hassadar kai wa ga wannan matsayin  sai wadanda ke son a ce su ne aka nada don su samu sukunin kudancewa cikin ruwan sanyi.
Duk da cewa Idris ya zo ne a lokacin da aka ci laggon ’yan ta’adda masu tayar da kayar baya, musamman takadaran yankin Arewa-maso-Gabas akwai abubuwan da zai ci karo da su, wadanda kuma suka dade suna wahalar da jama’ar kasar nan, kamar dambarwa tsakanin manoma da makiyaya  da  gawurtar rikice-rikicen yankin Neja Delta  da satar danyen mai da farfasa bututun man da ake hakowa da kuma tsohuwar sana’ar satar bil-adama da aka kasa magancewa  hade da fashi da makami da kuma fyaden da ake yi wa matan da ba su  san  hawa,  ba su san sauka ba.
Amma matsayinsa na matakin farko wajen inganta harkokin tsaro, aikin dansanda  na da wasu matsaloli na musamman da yake fuskanta.  Ba zai yiwu ba a ce ’yan sanda za su gudanar da ayyukan da suka fi karfinsu, ko wadanda ba su da karfi ko iko da kuma wadatattun kayayyakin aiki.  Kusan sulusin (daya bisa ukkun) yawan ’yan sandan kasar nan ba su yin aikin kare lafiya da rayuka  da dukiyar jama’a, domin kuwa a kan tuttura su ne  gidajen wasu hamshakan ’yan kasa don kula da  dukiyarsu da kuma kare lafiyarsu da mutuncinsu, don kada wadanda  suke zalunta su far musu a banza.Wannan ne ya sa ake karancin ’Yan sandan da za su wanzar da ayyukan da suka dace don biyan bukatun mutanen kasar nan  sama da miliyan  170. Shi ya sa ma ake zaton cewa karin ’yan sanda dubu 10 da Gwamnatin Muhamadu Buhari ke shirin yi a halin yanzu ba zai je ko ina ba wajen magance matsalolin da karancin ’Yan sanda   ke hadasawa a kasar nan.
Baicin karancin ’Yan sanda kuma akwai matsalar karancin kayayyakin aiki,  abin da ke sanyawa suna tserewa idan suka yi arangama da miyagun mutanen da ke karya doka,  wadanda suke da muggan makaman da ko sojoji ba su da su. Ashe ke nan ba abin mamaki ne ba  idan aka ga ’Yan sanda na rantawa-a-na-kare sa’ilin da  aka bude musu wuta, ko idan sun jinkirta zuwansu wuraren da miyagun ke sheke ayarsu har sai sun ci kasuwarsu, sun warwatse tukuna, sa’anan su iso suna mazurai da zazzare ido, da murza gashin baki, wai ga jarumai nan sun iso.  A wasu lokutan ma ko da mutanen da aka kai wa farmaki sun buga wa ’Yan sandan waya ba su dauka, haka nan za ta gaji da bugawa har ta yi shiru. Kai matsalololin da  ke hana ’yan sanda kumari na da yawan gaske, sun kuma hada da rashin karfafa gwiwa da rashin nakaltar makaman aiki da karancin albashi da kuma rashin kula ta musamman wajen horar da su yadda ya kamata. Wadannan abubuwa ne da ya kamata sabon Sufeto-Janar ya hanzarta magancewa kafin su kara yin kamari, har su faskara.
Dangane da wadannan dalilan ne ’Yan sanda, maza da mata da ake tura su wajen hamshakan masu kudi da kuma fitattun ’yan siyasa ba su komawa barikinsu,  duk kuwa da umurnin da  shugabanninsu suka yi ta bayarwa a lokutan baya. Irin wadannan ’Yan sandan ne ake yawan gani suna zuwa sautu, wasu ma har kawalanci suke yi; wasu kuwa sun zame babba-da -jakar maigidansu, wacce za su yi ta kinkimarta inda duk aka nufa;  wasu kuma jakar uwargidansa za su saba, kamar zabirar wanzami, suna bin ta zoi-zoi. Wasu ’yan siyasar ma  razana abokan adawarsu suke yi da ’Yan sanda da sukan cinna wa wadanda ke yi musu wani gani-gani; wasu kuwa  yawo suke yi da ’yan sandan don a ce sun isa.  
To, dandage da haka wajibi ne Idris ya dauki matakan dawo da irin wadannan ’yan sandan da ’yan siyasa suka sangarta cikin ’yan uwansu, domin su sha wuyar da ake sha tare da su. Hakan kuma zai bayar da damar kara yawan ’Yan sandan da za su kare lafiya da dukiyar talakawa .
Baicin haka nan ma sabon Sufeto-Janar din na da jan-aiki a gabansa na yin gyararrakin da suka dace don dawo da martabar aikin dan sanda. A ’yan shekarun baya dai kurar ’Yan sanda ta yi kuka yayin da ake ta zarginsu da yi wa bayin Allah kisan-mummuke a sassa daban-daban na kasar nan.  Talakawa dai sun zura ido su ga yadda za a  farfado da darajar dan sanda  wanda zai kware bisa aikinsa, ya kuma biya bukatar mutanensa har ya kuma  zabura cikin hanzari don  tsare lafiyar talakawa da magance abin da zai kware su, sa’annan kuma ya kasance mutum mai saukin  kai da za a kira abokin kowa.
Ba makawa wannan sabon Sufeto-Janar din zai yi amfani da kaifin basirarsa da kuma kwarewarsa wajen  inganta ayyukan dan sanda  a wannan lokacin da kasar ke fuskantar tsauraran matsalolin da suke hana jama’arta walwala da walawa, har ma ta kai ba su iya sakata, su wala. Wajibi ne kuma kowa da kowa ya ba shi cikakken goyon bayan da zai kai shi ga nasara  har ya sauke nauyin da aka dora masa.  An dai ce sabuwar tsintsiya ta fi dadin shara, amma sai idan ta kasance a hannun mutumin da ya san abin da yake yi.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos