Sabuwar wahalar man fetur ta kunno kai a Legas

Dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai a jihar Legas sun dawo sakamakon karancin man a garin, a daidai lokacin da wasu ke zargin gidajen da boye shi. A ranar Litinin ce dai mutanen jihar suka wayi gari da ganin dogayen layukan motoci a gidajen mai sakamakon karancinsa. Gwamnati ta cire hannunta a sanya farashin […]

Sabuwar wahalar man fetur ta kunno kai a Legas

PIC.4. FUEL HAWKER POPULARLY KNOWN AS BLACK MARKETERS HAVING A FIELD DAY AT FADEYI
AREA OF LAGOS ON THURSDAY (21/5/15) .
2673/21/5/2015/JAU/NAN

Dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai a jihar Legas sun dawo sakamakon karancin man a garin, a daidai lokacin da wasu ke zargin gidajen da boye shi.

A ranar Litinin ce dai mutanen jihar suka wayi gari da ganin dogayen layukan motoci a gidajen mai sakamakon karancinsa.

Wakilinmu ya lura cewa gidajen mai kalilan ne suka bude kuma suke sayar wa ga jama’a, yayin da yawancin suke kulle, ko ba su da shi gaba daya, ko kuma sun boye shi.

A wani gidan mai na kamfanin NNPC, wakilinmu ya lura akwai man, amma sun ki su sayar wa masu ababen hawan da suka hau layi tun misalin karfe 5:00 na Asubah.

Gidan man mallakin kamfanin NNPC da ke kan titin Ogunnusi, a Ojudu-Berger, masu motoci sun nuna fushinsu matuka kan yadda aka ki a sayar musu da man, bayan tabbacin da akwai.

Sun sanar da masu motoci cewa za su soma sayar da man da karfe 10:00 na rana, bayan kullum da karfe 7:00 na safe suke soma sayarwa.

A hirar da waikilin mu ya yi da wani mai mota, ya ce, a ranar Lahadi ana cikin sayar da man, haka kawai aka tsayar, a bisa umarnin Manajan gidan, “Wai hayaniya ta yi yawa. Mun yi ta rokonsa kan ya taimaka”

“Daga baya ya ce, mu dawo da karfe 6:00 na safiyar Litinin. Amma tun karfe 5:00 muke nan, sai suka ce sai karfe 10:00 , kuma babu wata hujja da suka bayar ta yin hakan,” in ji mutumin.

Ana zagrin gidajen man dai da karbar cin hancin N1,500 a kan jarka mai lita 30 kafin su sayar wa masu amfani da shi.