Sabuwar wakar Rarara ta sake yamutsa hazo

Sabuwar wakar Rarara ta sake janyo cece-kuce

Sabuwar wakar Rarara ta sake yamutsa hazo

Wata sabuwar waka da fitaccen mawakin siyasar nan Dauda kahutu Rarara ya fitar ta janyo ce-ce-ku-ce a kafofin sada zumunta.

Cece-ku-cen ya fi kamari ne a tsakanin magoya bayan jam’iyyar  NNPP, wadanda ke ganin wakar mai taken ‘Tsula Ya Sallama,’ a matsayin cin mutunci ce ga madugunsu, Rabiu Musa Kwankwaso.

Cikin wakar dai, Rarara ya bayyana yadda Kwanwason ya gana da Tinubu a Faransa, inda ya ce hakan alama ce ta neman tudun dafawa, da kuma kamun kafa don ceto kujerar dan takararsa, Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da Abba Gida-gida.

Sa’o’i kadan da fitar wakar, ta karade kafofin sada zumunta, inda Kwankwasawan suka hau sukar ta, cikinsu kuwa har da fitattun ’yan masana’antar Kannywood.

A shafinsa na Instagram, Mustapha Naburaska da a baya ke jam’iyya daya da Rararan ya yi Allah wadai da wakar, inda ya ce cin mutunci ce ga madugunsu Kwankwaso, don haka kada magoya baya su kyale Rararan.

“Kowa ya gaji bai saba ba, don haka idan ba ka gaji ba, mu ma ba za mu gaji ba, tun da ka yi sabuwar waka ka saki daya, sai mun maka gyara da guda tara.

“Duk dan Kwankwasiyya na duniya yanzu ya sani ga shi wannan mutumin ya kara taba uba a gare mu, maulana injiniya Dokta Rabiu Musa Kwankwaso.

“Wannan marokin ya sake sabuwar waka ya kuma taba shi. Ya sayi daya a yi masa gyara da guda tara,” in ji shi.

To sai dai duk da wannan ca da ’yan Kwankwasiyyar suka yi wa mawakin, hakan bai hana APC murna da wakar ba, inda Aminiya ta ci karo da wakar a shafin jam’iyyar na Faceebook reshen Jihar Kano.

“Mu dan shakata da Wannan ; Gari ya yi Gari Tsula ya sallama,” a cewar shafin.

Idan za a iya tunawa dai kwanaki kadan bayan bayyana sakamakon zaben Gwamnan Kano da NNPP din ta lashe, wasu bata-gari suka kona gida da ofishin Rararan da ke Kano.

Wasu dai na ganin hakan yana da alaka da kalaman da yake jifan Kwankwason da ba su yi wa magoya bayansa dadi ba.