Sace-sacen shanu ke kawo matsalar tsaro a Jihar Filato – Bature bincent

Kwamandan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (NSDSC) a Jihar Filato, Mista Bature bincent ya ce sace-sacen shanu ne babbar matsalar da ke barazana ga tsaro da ake fuskanta a halin yanzu a jihar. Kwamandan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Jos, inda ya ce a kullum suna samun […]

Sace-sacen shanu ke kawo matsalar tsaro a Jihar Filato – Bature bincent

Mista Bature Vincent Kwamandan NSDSC na Jihar FilatoKwamandan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (NSDSC) a Jihar Filato, Mista Bature bincent ya ce sace-sacen shanu ne babbar matsalar da ke barazana ga tsaro da ake fuskanta a halin yanzu a jihar.
Kwamandan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Jos, inda ya ce a kullum suna samun rahotannin sace-sacen shanu a jihar, amma jami’ansu tare  da sojoji da ’yan sanda suna  iyakar kokarinsu wajen magance matsalar sace-sacen shanun don dorewar zaman lafiya a jihar.
Mista Bature ya ce, “aikinmu shi ne tsaron rayukan jama’a don haka a nan Jihar Filato muna nan a cikin rundunar samar da tsaro ta musamman (STF) da rundunar tsaro ta gwamnatin Jihar Filato (Operation Rainbow) da tsare wuraren da bututun mai ya ratsa don ganin mun tsare sace-sacen mai da ake yi.
Kwamandan ya ce suna  lura da kayayyakin kamfanin ba wutar lantarki na kasa (PHCN) domin hana sace kayayyakin da barayi suke yi, sai kuma  tsaron bankuna tare da kula da wuraren da ake bukukuwa don bayar da tsaro.
Ya ce duk ayyukan samar da tsaro da wani kokari da ake yi na ganin zaman lafiya ya tabbata a jihar tare da su ake yi. Ya gargadin jami’an hukumar su rike aikinsu da kyau musamman ganin yadda gwamnati ta rike hukumar ta hanyar biyan ma’aikatanta hakkokinsu.