Sace ’yan matan Chibok: Akwai lauje cikin nadi

Kabir Sakaina Layin ’Yangoro Malumfashi (08095968366) ya aiko da sharhin cewa:Yanzu makonni biyu ke nan tun bayan da aka sace dalibai ’yan mata a garin Chibok da ke Jihar Borno, wadanda har yanzu ba a san halin da suke ciki ba. Abin bakin ciki da takaici, sai ga labari nata yaduwa cewa an tsallaka da […]

Sace ’yan matan Chibok: Akwai lauje cikin nadi
Sace ’yan matan Chibok: Akwai lauje cikin nadi

Kabir Sakaina Layin ’Yangoro Malumfashi (08095968366) ya aiko da sharhin cewa:
Yanzu makonni biyu ke nan tun bayan da aka sace dalibai ’yan mata a garin Chibok da ke Jihar Borno, wadanda har yanzu ba a san halin da suke ciki ba. Abin bakin ciki da takaici, sai ga labari nata yaduwa cewa an tsallaka da wasu daga cikinsu ta tafkin Chadi.
Bayan kuma a makon jiya ne muka ji labari na yaduwa cewa wadanda suka sace matan suna auren wasu daga cikinsu. Abin kamar almara! Tun iyayen yaran na sa ran jami’an tsaro za su iya kubutar da ’yayan nasu har suka fara mika lamarin ga Mai-yin-yadda-ya-so.
Don Allah ina jami’an tsoron Najeriya? Mene ne aikinsu? Ko dai zargin rashin kwarewar da ake masu a kan aikinsu gaskiya ne? Shin ta yaya wasu wadanda ake zargin ba a san ko su wane ne ba za su shigo cikin makaranta su saci akalla mata 200, ba tare da an gan su ko an san su ba? Gaskiya akwai lauje a cikin nadi, domin satar mutum 200 ba satar miliyan biyu ba ce.
Yau da a ce sarakuna, gwannoni, sanatoci da shuwagabannin al’umma za su yi koda barazanar bin barayin matan ne (kamar yadda iyayen daliban suka yi), na tabbata da jami’an tsaro sun dauki abin da muhimmanci. Amma a cikinsu babu wanda ya yi koda dogon kashedi ga jami’an tsaron, ballantana su dauki abin da mahimmanci.
Mun tabbata da a ce akwai ’yayan wani sarki, gwannan ko sanata, da yanzu an sa jami’an tsaro sun shiga dajin tun kafin a tsallaka da matan zuwa Chadi, duk kuwa da ake cewa dajin ko da rana sai ansa fitila.
Daga karshe, ya kamata jami’an tsaro tun daga kan sojoji da ’yan sanda su san cewa kare rayuka, dukiyoyi da mutuncin al’umma a karkashin su yake. Kamar yadda suke kare lafiya, dukiya da rayukan sarakuna, gwamnoni da sanatoci, to haka ya kamata su rika kare na talakawa. Ya Allah Ka bayyanar da matan da aka sace, Ka zaunar da kasarmu lafiya, Ka kare mu daga dukkan bata gari, Ka ba mu shugabanni adilai, amin!
***
Sanarwa: Masu bukatar rijistar kungiyar Gizago su tarba makon gobe in sha Allah.