Sace ’yan matan sakandaren Dapchi: Yaushe jami’an tsaro kowa zai tsaya aikinsa

Tun bayan harin da aka kai Kwalejin Ayyukan Gona ta Buni-Yadi da ke  Jihar Yobe cikin shekarar 2014, harin da ya yi sanadiyyar hallaka dalibai da dama da kuma na Sakandaren ’Yan mata ta Chibok a Jihar Borno shi ma a cikin shekarar 2014, inda aka sace ’yan mata sama da maitan da hamsin, wadanda […]

Sace ’yan matan sakandaren Dapchi: Yaushe jami’an tsaro kowa zai tsaya aikinsa

Tun bayan harin da aka kai Kwalejin Ayyukan Gona ta Buni-Yadi da ke  Jihar Yobe cikin shekarar 2014, harin da ya yi sanadiyyar hallaka dalibai da dama da kuma na Sakandaren ’Yan mata ta Chibok a Jihar Borno shi ma a cikin shekarar 2014, inda aka sace ’yan mata sama da maitan da hamsin, wadanda har yanzu mahukuntan kasar nan ba su ceto dukansu ba. Hare-haren da ake kyautata zaton kungiyar Jama’atu Ahlis Sunnah Lid’ Da’awati Wal Jihad da aka fi sa ni da Boko Haram suka kai su. Haka kwatsam kuma sai ga wani hari daga bangaren Albarnawi na kungiyar ta Boko Haram sun kai ga Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta ’Yan mata ta garin Dapchi a  Jihar Yobe a ranar Litinin 19-02-2018, inda zuwa yanzu rahotannin mahukunta suka tabbatar da cewa ’ya’yan kungiyar sun sace ’yan mata 110, daga cikin ’yan mata 926, da suka tarar a makarantar da magariba. 

Kamar yadda aka samu cece-ku-ce tsakanin mahukunta na jami’an tsaro da gwamnatoci a kan gaskiya ko rashin gaskiyar sace ’yan matan Chibok a wancan lokaci, a wannan karo ma haka aka fara kwatawa. Ta yadda Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya yi zargin cewa kwashe jami’an tsaron da aka yi daga garin Dapchi da ke yankin Gaidam kusan mako daya kafin kai harin, shi ya bude kofa ga ’yan kungiyar Boko Haram har suka kai harin. Yayin da sojoji suka ce kafin su bar garin Dapchi, sai da su ka mika tsaron garin ga hannun ’yan sandan yankin, zargin da Rundunar ’Yan sandan Jihar Yobe ta bakin Kwamishinanta ta musanta. 

Bisa ga al’ada, duk lokacin da aka samu irin wannan sakaci da aiki da yakan kai ga aikata danya irin wannan musamman a makarantu za ka ga a cikin kasa da wajenta an yi ca ana kokawa cewa sakacin mahukunta ya kawo haka, ba don komai ba sai don kasancewar dalibai da aka dauka aka raba su da gidajen iyayensu zuwa makarantu da zimmar koya musu ilmi, a kuma wayi gari a ce an kai musu hari wadansu a kashe su wadansu kuma a sace su kamar yadda aka  yi a Kwalejin Ayyukan Gona ta Buni-Yadi da Makarantun ’Yan mata ta Chibok da Dapchi a jihohin Yobe da Borno, yakan zama abin kunya da kasawar mahukunta, kasancewar tamkar gwamnatocin sun kasa tsare amanar ’ya’yan jama’a kamar yadda suka dauka. Alal misali, tunda aka fara rikicin Boko Haram a shekarar 2009, Allah kadai Ya san yawan maza da mata manya da kanana da ’yan kungiyar ta Boko Haram suka sace, kamar yadda yanzu da yaki da ’yan kungiyar ta Boko Haram ya yi kamari sojoji suna ta kubutar da daruruwan irin wadancan mutane daga hannun kungiyar ta Boko Haram amma ba wanda ya mai da hankali a kan sace irin wadancan jinsin mutane kamar yadda yanzu duniya ta yi ca, a kan sace ’yan matan na makarantun sakandaren Chibok da Dapchi. 

Alal misali bayan harin da aka kai a Kwalejin Ayyukan Gona ta Tarayya, Buni-Yadi da sace ’yan matan Chibok da aka yi dukansu a shekarar 2014, ya sanya a wani taron duniya a kan tattalin arzikin Afirka da aka yi a Abuja ranar 7-05-2014, Shugaban kasa mai ci a wancan lokacin Dokta Goodluck Jonathan da Jakadan Majalisar dinkin Duniya a kan fannin ilimi na duniya kuma tsohon Firayi Ministan kasar Birtaniya Mista Gordon Brown da wadansu manya ’yan kasuwar kasar nan sun kafa wani kwamiti da aka dora wa alhakin bullo da tsarin da zai tabbatar da tsaro a dukan kwalejoji da makarantun jihohin Borno da Yobe da Adamawa, jihohin da nan rikicin kungiyar ta Boko Haram ya fi kamari. An kaddamar da wani karamin kwamiti a ranar 17-07-2014, da aka dora wa alhakin tabbatar da cewa makarantun shiyyar suna cikin tabbataccen tsaro da zai samar da yanayin walwala da jin dadi ta yadda koyo da koyarwa za su samu cikin kwanciyar hankali. 

Mambobin babba da karamin kwamitin sun hada da gwamnonin jihohin Borno da Yobe da Adamawa da Ministan Ilmi da ta kula da harkokin mata da sauran masu ruwa-da-tsaki, kwamitocin da suka samu gudunmawar kudi daga Gwamnatin Tarayya da ta kasar Jamus da Bankin Raya Afirka da kungiyoyin bayar da tallafi na kasa da kasa. Mai karatu ka iya cewa yanzu kake jin labarin kafa wadancan kwamitoci don tabbatar da tsaro a makarantun wadancan jihohi, kwamitocin da tun daga wancan lokaci gwamnatin Shugaba Jonathan da ta yi gaba-gaban kafa shi da ta tsaya a kansa, to kuwa kila yau da wancan hari da sace ’yan matan na Dapchi da aka yi, da ba a yi shi ba. Amma kowa ya san irin yadda gwamnatin tsohon Shugaban kasa Jonathan da makarrabanta suka rika jan kafa da ma musanta an sace ’yan matan na Chibok, don haka ne ma yakar kungiyar ta Boko Haram ya zama cikin kila-wa-kala, wato babu wata cikakkiyar kulawa har sai da wannan gwamnati ta Shugaba Muhammdu Buhari ta zo kan karagar mulki a shekarar 2015, kusan shekara 6, ana fama da wannan rikici.

Koda yake a kai hari da sace ’yan makarantar na Dapchi an so a kwatanta abin da ya faru a kan na Chibok din, a lokacin da Gwamnan Jihar Yobe da ita kanta ta Gwamnatin Tarayya da jami’an tsaronta, da farko sun nemi su musanta sace ’yan matan na Dapchi amma kuma daga bisani suka fahimci gaskiyar lamari abin da ya kai ga Gwamnan Jihar Yobe da shi kanshi Shugaban kasa suka nemi afuwar iyayen yaran da al’ummar kasa baki daya a kan abin da ya faru da makarantar ta Dapchi. A gefe daya kuma mashawarci ga Shugaban kasa a kan Harkokin Tsaro, Manjo Janar Babagana Mongunu zuwa yanzu ya kafa wani kwamiti na mutum 12, da ya dora wa alhakin bin diddigin yadda aka kai harin na Dapchi da kuma irin rawar da jami’an tsaro suka taka cikin al’amarin baki daya a cikin garin na Dapchi da makarantar kanta da irin yadda za a iya ceto ’yan matan. An dai ba kwamitin wa’adin nan da 15 ga wannan wata na Maris ya mika rahotonsa. Ita ma Majalisar Wakilai ta kafa nata kwamitin na musamman da zai yi mata bincike a kan wancan hari na makarantar ta Dapchi, kwamitin da ta ba nan da mako 4, ya mika mata rahotonsa.

Jami’an tsaro sun ce zuwa yanzu sun baza komarsu zuwa cikin kasashen makwabta irin su Jamhuriyar Nijar da Chadi don neman ’yan matan. Ko yaya ka kalli yadda aka sace ’yan matan na Dapchi a daidai lokacin da sojoji suka mayar da karfinsu wajen yakar ’yan Boko Haram a lungunan Jihar Borno inda nan annobar ta fi kamari, ka iya cewa akwai sakaci da har jami’an tsaron suka kasa gane cewa yaki dan zamba ne, kuma shi abokin fada ko kusa ba ka sarara masa. Abin da dai ya riga ya faru ya faru a makaranatar ta Dapchi, saura da me? Yanzu sai ’yan kasa a ci gaba da addu’o’in Allah Ya bayyana wadancan ’yan mata na Dapchi, da ma sauran na Chibok tare da kawo karshen rikicin Boko Haram baki dayansa. Mahukunta kuma musamman jami’an tsaro su kara mayar da hankali wajen aikinsu.