Sadaukan malamai suka gina al’umma
Malamai na kukan talauci, musamman albashinsu ba wani ba ne, idan aka kwatanta da sauran ma’aikatun kasar nan. Wannan matsalar ba ta raba tsakanin malaman makarantun Firamare da Sakandare da Jami’a ko malaman addini ba. Kuma abin bai tsaya a kan rashin biya kan lokaci ba. Ba a kara musu girma. Hakan ya kara bata […]
Malamai na kukan talauci, musamman albashinsu ba wani ba ne, idan aka kwatanta da sauran ma’aikatun kasar nan. Wannan matsalar ba ta raba tsakanin malaman makarantun Firamare da Sakandare da Jami’a ko malaman addini ba. Kuma abin bai tsaya a kan rashin biya kan lokaci ba. Ba a kara musu girma.
Hakan ya kara bata aikin ko sana’ar koyarwa, ta yadda ake gudun aikin, ko an fara da zarar wata dama ta samu sai a yi gaba, kuma hakan na faruwa duk da cewa akwai hukumomi da ma’aikatu da aka kafa don kulla da harkokin da suka shafi ilimi a kasar nan.
Wani abin sai mutum ya kai ziyara inda ake shake yara sama da dari a aji daya, wannan ya sa masu dabara ke koyar da yara har a gida don su biya bukatunsu da na iyalai a karshen wata. Shi ya sa a halin yanzu ya wajaba malaman jami’a su tafi da bukatun Firamare da Sakandare, sai a farfado da ilimi, kasa ta ci gaba.
Ta wata fuskar manazarta da dama na kallon halin da malamai suka shiga yana da nasaba da adawarsu da ‘yan siyasa, domin wani dan takarar da malam ya koyar, sai ya zo rana tsaka ya mallaki duk kudin da malamin ya mallaka a rayuwarsa a wata daya!
Duk da ‘yan siyasa suke karya da karin karya, suka mayar da kansu mayaudara, musamman domin irin alkawuran da ake dauka kafin a ci zabe. Bayan an lakuta wa mutane zuma a baka, sai a fara harbinsu! Wai da albashin malaman za a gyara makarantun? Shin akwai niyyar zamanantar da harkokin ilimi a kasar nan. Maimakon ya zama akwai gasa tsakanin makarantun kudi da na gwamnati, a nan kasar komai na gwamnati shi ne koma baya, makarantu da asibitoci da shaguna da gidaje da da an samu gwamnatin wata jiha, wadda da gaske take da makarantunta sai sun fi na masu zaman kansu, wai wa ya kai gwamnati kudi?
An sha maganganu da bayanai da rubuce-rubuce game da halin da ilimi ya fada a kasar nan, amma maimakon matsalolin su zo karshe, sai kara kaimi suke yi, matsalolin ilimi sun ratsa kowane mataki. Tabbas babu kwakwaran mataki da ake dauka wajen warware wannan matsalar. Abin da yake damun malami, yana damun kowa!
Haramta makarantun boko masu zaman kansu ba matakin da zai inganta ilimi ba ne. Kuma duk inda ilimi ya inganta, malamai nagari aka samu ingantattu, hakan ke haifar da dalibai masu nagarta, manyan gobe wadanda za su gina kasa.
Abin takaici ne shugabanni sun dauki malamai kamar wasu fitinannu, ilimin kamar wani bangare da ke tsotsar haraji, duk da cewa malamai ne na karshen karbar albashi a kowane wata. A koyar, kai ya waye.
Masu koyarwa a makarantun kudi wani lokaci suna samun sauki, domin su ma sai ka iske makarantar da karbar kudi, dalibai na biya da tsada, amma ana biyan malaman makarantar alakoro, saboda rashin aikin yi a kasar sun gaza barin makarantar! Ita kanta kungiyar malamai (NUT) da kungiyoyin iyayen dalibai da malamai (PTA) ya kamata su fito a fafata. Wani abin dubawa shi ne duk malamin da ya yi ritaya sai a bar shi a layin neman fenso ko giratuti, karin girma ya gagara sai a kafe da ba ofis ko inda za a makala malami! A kasashen da ake daraja ilimi, malamai waje ake musu, talakawa kan yi burin zama malamai.
Sau da yawa gyara makaranta, watau a yi mata fenti ko kwaskwarima ba su kara wa malaman komai, ita kanta makarantar kwaliya ake yi wa ta kan hanya! Ko a watsa mata fentin jam’iyyar da ke mulki, dalibai su rasa idan aka samu canjin gwamnati, me zai faru? Domin sai ka shiga makaranta ba kayan aiki, sai a rika ihun an gyara makarantu, wai an farfado da ilimi. Bayan a zahiri darajar ilimi ta fadi a kasar nan, musamman don malamai ba su da kima wajen tafiyar da kasa, duk da cewa a tashin farko ‘yan siyasar da suka gina kasar malamai ne, domin a da can an san darajar maluma, malamai ya kamata a rika kira honorobul, ba masu tambarin yaudara ba watau ‘yan siyasar Najeriya! Kuma tabbas nasarar ASUU, nasarar talakawan Najeriya ce. Gara gwamnati ta daidaita sahu don a koma makaranta. Idan kasar nan za ta farfado dole a ba ilimi malamai za a ba iwa muhimmanci, ta yadda za su zama wakilai, su share mana hawaye. Amma abin takaici sai ka iske wadanda ba su da ilimi ko wayewa su ne wakilai, mutanen da ba su da ilimin addininmu, ba su iya mu’amala ba, a ce su ne shugabanni! Sannan sai ka iske wanda ba ya da baiwar koyarwa ya zama malami, tabbas hakan kissan kai ne, ya zama malami a dalilin bai samu wani aiki ba. Ko an ki, ko an so ‘ci gaban malaman makaranta ne ginin al’umma.’ Malamai sun fi likitoci muhimmanci, domin malaman suka koyar da likitocin, a haka mun tabbatar da ba da ingantaccen ilimi ya zama burin kowace gwamnati a aikace, ta yadda za a dora al’umma a kan tarbiyya. [email protected]