Sadaukarwar ’yan Najeriya ba za ta tafi a banza ba — Tinubu

Tinubu ya ce kasafin na 2025 zai mayar da hankali wajen bunƙasa tattalin arziƙin Najeriya.

Sadaukarwar ’yan Najeriya ba za ta tafi a banza ba — Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa sadaukarwarsu za ta haifar da sakamako mai tasirin gaske nan ba da jimawa ba.

Tinubu, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin gabatar da kasafin kuɗin Naira tiriliyan 47.9 na shekarar 2025 ga majalisun dokoki ƙasa.

Tinubu, ya aminta cewar watanni 18 na gwamnatinsa sun kasance masu wuya, amma ya roƙi ‘yan Najeriya su ci gaba da yin haƙuri.

“Aikin bunƙasa tattalin arziƙi da ci gaba, wanda muka fara watanni 18 da suka gabata a matsayin ƙasa, yana ci gaba da tafiya,” in ji shi.

“Babu wata hanya da ta dace mu zaɓa, hanya ɗaya ce da dole muka ɗauka domin Najeriya ta samu damar zuwa wani babban mataki.

“Na gode wa kowane ɗan Nijeriya da yake tafiya tare da mu a wannan tafiya ta gyara.”

Ya ƙara da cewa, “Hanyar gyaran a yanzu tana samar da kyakkyawan sakamako sosai, kuma a matsayina na shugaban wannan ƙasa mai albarka, na san cewa wannan hanya ba ta kasance mai sauƙi ba.

“An sha wahalhalu. Kuma hakan ba zai tafi da banza ba. Dole ne mu ci gaba da amincewa da tsarin domin cikar burinmu.”

Kasafin kuɗi na 2025, kamar yadda Tinubu ya bayyana, na nufin ɗorawa kan ayyukan da gwamnatinsa ta faro watanni 18 da suka gabata.

Har ila yau, ya ce gwamnatin za ta mayar da hankali kan sake tsara hanyoyin bunƙasa tattalin arziƙi, ilimi, bunƙasa kasuwanci da sauransu.

Ya sake jaddada burinsa na ganin tattalin arzikin Najeriya, ya bunƙasa tare da yin gogayya da manyan ƙasashen duniya.

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira