Sadio Mane ya koma Al Nassr ta Saudiyya
Mane ya koma Al Nassr ne bayan raba gari da Bayern Munich.
Tsohon dan wasan gaban Liverpool, Sadio Mane, ya raba gari da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich, inda ya koma kungiyar Al Nassr da ke Saudiyya.
Mane dai a yanzu zai rika daukar albashi Yuro 650,000 duk mako a sabuwar kungiyarsa.
- Ba za mu lamunci tashin hankali yayin zanga-zanga ba -Sufeton ‘Yan sanda
- Akwai yiwuwar kungiyar kwadago ta dage zanga-zangar da ta shirya yi ranar Laraba
Ya rattaba hannu a kan kwantiragin kuma zai ci gaba da zama a kungiyar har zuwa karshen kakar wasa ta 2027, inda zai dauki jimillar kudi Yuro miliyan 136.
Yanzu dai Mane zai hade da Cristiano Ronaldo, Alex Telles, Marcelo Brozovic da sauran ’yan wasa da suka sauya sheka daga nahiyar Turai zuwa Saudiyya.
Sadio Mane ya sauya sheka daga Liverpool zuwa Bayern Munich a kakar da ta wuce kan kudi Yuro miliyan 35, amma ya samu matsala da dan wasa Leroy Sane.
Kafin barin Liverpool, Mane ya buga wasanni 269, inda ya zura wa kungiyar kwallo 120.