HotunaKiwon Lafiya• Created May 17, 2020 19:01
HOTUNA: Sadiya Farouk ta mika tallafin abinci ga gwamnatin Kano
Ministar Jinkai da Agajin Gaggawa, Sadiya Umar Farouk, ta mika kayan abinci tirela 120 ga gwamnatin Kano, a matsayin tallafin gwamnatin tarayya ga jihar domin rage wa al’umma radadin dokar zaman kulle mai muradin hana yaduwar coronavirus. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya karbi kayan a madadin al’umar jihar a ranar Lahadi.
Ministar Jinkai da Agajin Gaggawa, Sadiya Umar Farouk, ta mika kayan abinci tirela 120 ga gwamnatin Kano, a matsayin tallafin gwamnatin tarayya ga jihar domin rage wa al’umma radadin dokar zaman kulle mai muradin hana yaduwar coronavirus.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya karbi kayan a madadin al’umar jihar a ranar Lahadi.
Ministar Jinkai da Agajin Gaggawa, Sadiya Umar Faruk tare da Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a lokacin da suke kewaya kayan abincin tallafi da ta mika wa Gwamnatin jihar Kano
Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, tare da Hajiya Sadiya Umar Farouk, Ministar Jinkai da Agajin Gaggawa, a lokacin da ta mika tallafin abinci sama da tirela 100 ga gwamnatin jihar Kano
Wasu daga cikin kayan abincin sama da tirela 100 da Ministar Jinkai da Agajin Gaggawa, Sadiya Umar Farouk, ta mika wa gwamnatin jihar Kano
Wani sashe na kayan abincin da Ministar Jinkai da Agajin Gaggawa, Sadiya Umar Farouk, ta mika wa gwamnatin jihar Kano. (Tsohon hoto)
Nan ma wasu daga cikin kayan da Ministar Jinkai da Agajin Gaggawa ta mika wa gwamnatin jihar Kano ne
Sadiya Umar Farouk, Ministar Jinkai da Agajin Gaggawa, tare da Gwamnan Kano, Abudllahi Umar Ganduje, a lokacin da take jawabin mika masa kayan abinci da gwamnatin tarayya ta bai wa jihar
Ministar Jinkai da Agajin Gaggawa, Sadiya Umar Farouk, tare da Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a lokacin da suke duba abincin tallafi da ta mika wa Gwamnatin Kano
Wani bangare na kayan abincin da Ministar Jinkai da Agajin Gaggawa, Sadiya Umar Farouk, ta mika wa gwamnatin jihar Kano