Safiyya Ahmad ta lashe gasar Hikayata ta BBC Hausa

Bayan kammala gasar rubutun kagaggun labarai ta BBC Hausa wanda aka shirya don mata zalla. Alkalan gasar sun zabi Safiyya Ahmad da labarinta mai suna “Maraici” a matsayin wadda ta yi nasarar zama gwarzuwar gasar Hikayata ta 2019. Safiyya Ahmad ta lashe kyautar kudi dala dubu biyu, wanda yake kwatankwacin sama da Naira dubu dari […]

Safiyya Ahmad ta lashe gasar Hikayata ta BBC Hausa

Bayan kammala gasar rubutun kagaggun labarai ta BBC Hausa wanda aka shirya don mata zalla. Alkalan gasar sun zabi Safiyya Ahmad da labarinta mai suna “Maraici” a matsayin wadda ta yi nasarar zama gwarzuwar gasar Hikayata ta 2019.

Safiyya Ahmad ta lashe kyautar kudi dala dubu biyu, wanda yake kwatankwacin sama da Naira dubu dari bakwai.

Wadda ta zo ta biyu kuma ita ce Jamila Abdullahi Rijiyar Lemu, da labarinta mai suna “Ba a yi komi ba,” wacce ta karbi kyautar dala dubu daya.

Sannan labarin “A juri zuwa rafi” na Jamila Babayo shi ne ya zo a matsayi na uku, wacce ta karbi kyautar dala dari biyar.

An karramar marubutan ne da labaransu suka yi fice a wani gagarumin taro da fitattun mutane kama daga masu mulki da marubuta da jaruman fina-finai da masu kare hakkokin mata suka halarta a Abuja.

Wannan ne karo na hudu da Sashen Hausa na BBC ke karrama matan da suka yi nasara a gasar Hikayata tun bayan kaddamar da ita a shekara ta 2016.

Abin da ya sa labaran suka yi fice kuwa, a cewar jagorar alkalan Dokta Aliya Adamu, shi ne “Salo”.

Ta kara da cewa, “Salo dubara ce ta isar da sakonka; to wadannan gajerun labarai, duk da suna gajeru, marubutan sun yi amfani da wani salon a daga hankalin mai sauraro ko mai karatu, kuma su hukunta ko wane tauraro daidai da rawar da ya taka a cikin labarai”.

Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta kai wannan matsayi ne da labarinta mai suna “Ba A Yi Komai Ba”.

“Ba A Yi Komai Ba” labari ne a kan Uwani, wata mata da ke haifar ‘ya’ya mata—sakamakon haka mijinta da danginsa suka uzzura mata har dai daga karshe ya sake ta.

Ita kuma Jamila Babayo labarinta mai suna “A Juri Zuwa Rafi” ne ya kai ta wanna matsayi. Labarin dai na wata yarinya ce Aisha wadda wani mawadaci a unguwarsu ya yi mata fyade, sannan dangina gaba daya suka nemi a rufe maganar, amma mahaifiyarta ta ce sai ta kwato mata hakkinta.

Labarin “Maraici” kuwa, wanda da shi Safiyya Ahmad ta samu kaiwa wannan matsayi, yana magana ne a kan Karima—wata yarinya da ta taso a gidan marayu, daga baya ta samu uwar riko wadda ta aurar da ita, amma zaman auren ya gagara saboda wulakancin da take fuskanta sakamakon kallon da ake yi mata na mara asali.

 

Gwaraza uku na gasar Hikayata BBC Hausa 2019