Sahabbai Goma ’yan Aljannah (1)

Godiya ta tabbata ga Allah, Wanda Ya aiko Annabi (SAW) a matsayin rahama ga dukan halittu. Kuma Ya karfafa shi da wazirai amintattu su ne taurarin wannan al’umma. Tsira da Aminicin Allah su kara tabbata ga Annabi da alayensa da sahabbansa. Bayan haka, bayan mun dauki dogon lokaci muna gabatar da wani abu kan rayuwa […]

Sahabbai Goma ’yan Aljannah (1)
Sahabbai Goma ’yan Aljannah (1)

Godiya ta tabbata ga Allah, Wanda Ya aiko Annabi (SAW) a matsayin rahama ga dukan halittu. Kuma Ya karfafa shi da wazirai amintattu su ne taurarin wannan al’umma. Tsira da Aminicin Allah su kara tabbata ga Annabi da alayensa da sahabbansa.

Bayan haka, bayan mun dauki dogon lokaci muna gabatar da wani abu kan rayuwa da gwagwarmayar Manzon Allah (SAW), inda muka ce za mu dan dakata a makon jiya, a yau za mu fara duba wani abu kan rayuwar wadansu mutum goma daga cikin sahabbansa wadanda suka taimaka masa wajen isar da sakon Musulunci. Duk da cewa a takaice aka kawo tarihin wadannan sahabbai (Allah Ya yarda da su) akwai abubuwan da za mu tsinta da za su taimaka mana a rayuwarmu ta duniya da Lahira:

Gabatarwar Mawallafi

Godiya da yabo su tabbata ga Allah Madaukakin Sarki. Tsira da Amincin Allah, su tabbata ga fiyayyen talikai, Annabin Rahama, Muhammad (SAW) alayensa da sahabbansa.

Bayan haka, Allah Ya kawo mu wani zamani, wanda yin riko da addini da aiwatar da al’amuran rayuwar yau da kullum bisa koyarwarsa, ba a dauke su a bakin komai ba. Hasali ma wadansu su dauki yin haka kauyanci ne da gidadanci da rashin wayewar kai. Ga makarantun Alkur’ani da koyon ilimin addinin shake da dalibai a kowane sako na kasar nan, musamman jihohinmu na Arewa, amma kash! Amfani da abin da ake koyo ta hanyar aiwatar da shi, cikin rayuwar yau da kullum ya yi karanci ainun! Adalci ya karanta ga shugabanni, takawa da tsantseni, sun yi rauni ga malamai, tausayi ya gushe daga zukatan mawadata, hakuri da tawakkali, sun fice daga zukatan talakawa! Mun shiga wata irin bahaguwar rayuwa, wadda abin duniya, shi ne gaba da addini da mutunci da kimar dan Adam!

Bayan duk wadannan, ga kuma wata masifa da ta kunno kai, wadda take barazana ga imanin mutum. Ba kuwa wata aba ba ce, face bayyanar aibatawa da muzanta manyan sahabban Annabi (SAW) musamman ma halifofinsa uku na farko, wadanda suka taimaki Annabi (SAW) wajen sadaukar da rayuwarsu da dukiyoyinsu don daukaka addinin Allah da yada shi. Kuma tun kafin su bar duniya suka samu tikitin shiga Aljannah. Hakika wannan ba karamin hadari ne ga rayuwar duk wanda ya yi riko da wannan mummunar akida ba a duniya da Lahira.

Sakamako irin wannan hardaddiyar rayuwa da muka tsinci kanmu a cikinta a yau, muka ga ya dace mu rairayo tarihin wadansu sahabban Annabi (SAW) goma wadanda ya yi wafati suna yardaddu ga Allah kuma yardaddu a gare shi (SAW), wadanda kuma ya yi musu bushara da gidan Aljannah, domin mu ga irin sayar da rai da gwagwarmayar da suka sha, wajen tabbatar da addinin Allah a bayan kasa, saboda mu yi koyi da irin rayuwarsu, ko ma samu kasancewa cikin masu babban rabo a rayuwarmu ta duniya da ta gobe Kiyama. Muna rokon Allah Ya ba mu ikon koyi da rayuwar wadannan bayi naSa nagari, Ya kuma karbi wannan aiki da muka yi, Ya sanya mana shi a cikin mizanin kyawawan ayyukanmu.

  1. Sayyidina Abubakar Siddiku (Allah Ya yarda da shi):

“Ya Abubakar! Kai ne farkon wanda zai shiga Aljannah daga al’ummata,” inji (Manzon Allah SAW).

Sayyidina Abubakar shi ne Abdullahi dan Abu Kuhafatu (Usman) dan Amiru dan Ka’abu dan Sa’adu dan Taimum dan Murratu dan Ka’abu dan  Lu’ayyu. Bakuraishe, Batayime. Nasabarsa ta hadu da ta Manzon Allah (SAW) ta wajen Murratu dan Ka’abu, wato kakansu na biyar.

Sunansa a lokacin Jahiliyya; “Abdul Ka’aba” da ya Musulunta sai ya koma Abdullahi kuma Manzon Allah (SAW) ya yi masa alkunya da Abubakar saboda rigayensa wajen dabi’antuwa da kyawawan halaye. An kuma yi masa lakabi da “Assiddiku” saboda saurin bayar da gaskiyarsa ga duk abin da Manzon Allah (SAW) ya fada, haka Manzon Allah (SAW) ya kira shi da Atiku.

Shi ne mutumin da ya fara musulunta a maza manya. Shi ne mutum na farko da ya fara kira zuwa ga addinin Allah bayan Annabi (SAW). Shi ne ya fara huduba a addinin Musulunci. Shi ne abokin zaman kogo tare da Manzon Allah (SAW). Shi ne farkon sahabbai goma da aka yi wa bushara da gidan Aljannah tun a duniya. Shi ne farkon “Amirul Hajj.” Yana cikin marubuta wahayi ga Annabi (SAW).

An haifi Sayyadina Abubakar (RA) a Makka bayan Shekarar Giwaye da shekara uku (Shekara ta 573 Miladiyya), wato Manzon Allah (SAW) ya girme shi da shekara uku. Yana cikin manyan shugabannin Kuraishawa a lokacin Jahiliyya, abin so gare su. Abokin Manzon Allah (SAW) ne na kusa, tun kafin aiko shi. Sau da yawa ma, yakan je gidansa su tattauna. Shi ne mafi sanin dukan Larabawa game da tarihin nasabar Kuraishawa.

Ya kira mutane da dama zuwa ga addinin Musulunci, biyar daga cikinsu, suna cikin Sahabbai Goma da aka yi wa bushara da Aljannah. Su ne: Usman bin Affan da Zubairu bin Awwam da Abdurrahmanu bin Auf da Sa’adu bin Abu Wakkas da Dalhatu bin Ubaidullahi. (Allah Ya yarda da su gaba daya). Ya sha azaba iri-iri daga kafiran Makka saboda shigarsa Musulunci, har ta kai babu wani Musulmi da ya azabtu kamarsa (a manyan sahabbai).

Duk da irin matsananciyar azabar da suka sha shi da sauran Musulmin farko daga karfiran Makka, bai yi kaura zuwa kasar Habasha ba, yana tare da Manzon Allah (SAW). Lokacin hijira zuwa Madina kuma yana tare da Annabi (SAW) tare suka shiga kogo kafin su wuce zuwa Madina shi ne na cikon mutum biyu da Allah Ya ambata a Kur’ani, inda ya ce:

“Idan ba ku taimake shi ba, (Annabi SAW), to, ai Allah Ya taimake shi yayin da kafirai suka fitar da shi (daga Makka) yana biyun na (mutum) biyu, yayin da suka shiga cikin kogo, yana cewa da abokinsa (Abubakar) Kada ka ji tsoro! Hakika Allah Yana tare da mu, (da taimakonSa.)” (Tauba:40).

Yayin da suka isa Madina, Sayyidina Abubakar (RA) ya sauka a wurin Kharijatu dan Zaidu. Da shi kuma Manzon Allah (SAW) ya hada su ’yan uwantaka, yayin da ya rika hada ’yan uwantaka (ta Musulunci) a tsakanin mutane Makka (Muhajiruna) da na Madina (Ansaru). Sayyidina Abubakar shi ne tamkar waziri ga Annabin Musulunci, mai babbar hedikwata a Madina, Birnin Manzo (SAW).

Abubakar Siddik (RA), ya halarci dukan yake-yaken daukaka Musulunci da yada shi tare da Annabi (SAW). A Yakin Badar shi ne kan gaba wajen kula da wurin da Manzon Allah (SAW) yake, yana shirya gudanar da yakin tare da rokon Allah. Har dai Allah Ya amsa addu’ar Annabi (SAW), ya aiko da rundunar Mala’iku, Musulmi suka samu babbar nasara. A Yakin Uhudu kuwa, Sayyidina Abubakar (RA), shi ne jagoran tsirarin manyan sahabbai da suka tabbata a filin yakin tare da Manzon Allah (SAW) yayin da kafirai suka tarwatsa Rundunar Musulmi.

Kamar yadda Sayyidina Abubakar ya sadaukar da kansa ga Addinin Musulunci, haka ma ya mika dukiyarsa gaba daya wajen daukaka addinin Allah. Hasali ma, Manzon Allah (SAW) cewa ya yi “Ban taba amfanuwa da dukiya ba irin ta Abubakar.”

A lokacin da ya musulunta, yana da tsabar kudi Dirhami dubu arba’in (40,000). Amma duk ya bayar da ita ga hanyoyin Ubangiji daban-daban don daukaka Musulunci. Ya sayi bayi da dama wadanda kafiran Makka suke azabtarwa, saboda sun shiga Musulunci, ya ’yanta su kamar Bilal dan Rabah da Amiru dan Fuhaira da Zannira da wadansu da dama. Kan haka ne Allah Ya saukar da fadinSa:

“Mafi takawa zai nisance ta (wuta) wanda yake bayar da dukiyarsa, yana tsarkakuwa. Alhali babu wani mai wata ni’ima a wurinsa, (wani kyakkawan abu da yake so a yi masa) da ake neman sakamakonta, sai don neman yardar Ubangijinsa Mafi daukaka. Hakika kuwa zai yarda, (da sakamakon da za a ba shi a Lahira).” (Laili:17-21).

Imam Ahmad Adam Kutubi,  Nigeria Police Force, Zone 7, Police Headkuarter, Abuja. 08036095723