Sahabbai Goma ’yan Aljannah (5)

Sayyadina Umar (RA) ya sanya shi daya cikin mutum shida da ya ce su yi shawara, su zabi wanda zai zama halifa a bayansa daga cikinsu. Ya ce: “Su ne wadanda Manzon Allah (SAW) ya yi wafati suna yarddadu gare shi. Haka kuma yana cikin sahabbai goma da aka yi wa bushara da gidan Aljanna.” […]

Sahabbai Goma ’yan Aljannah (5)
Sahabbai Goma ’yan Aljannah (5)

Sayyadina Umar (RA) ya sanya shi daya cikin mutum shida da ya ce su yi shawara, su zabi wanda zai zama halifa a bayansa daga cikinsu. Ya ce: “Su ne wadanda Manzon Allah (SAW) ya yi wafati suna yarddadu gare shi. Haka kuma yana cikin sahabbai goma da aka yi wa bushara da gidan Aljanna.”

Ya karbi wasiccin kula da iyalan wadansu daga sahabban Annabi (SAW) kamar Sayyadina Umar da Abdurrahaman dan Auf da Abdullahi dan Mas’udu da Mikdadu (Allah Ya yarda da su) ya zamo yana kula da dukiyarsu, yana kuma ciyar da su daga tasa dukiyar. An yi wa Sayyadina Zubairu kisan gilla yayin da yake Sallah a wani wuri da ake kira Kwarin Zakoki’. Ibn Jurmur ne ya kashe shi, har ma ya dauki takwabinsa ya kai wa Sayyadina Ali (RA). Sai (Sayyidina Ali RA) ya ce: “Sau daya wannan takwabi, ya yaye bakin ciki ga Manzon Allah (SAW)” Sannan ya ce: “Yi wa makashin dan Safiya (Zubairu RA) bushara da gidan wuta!”

An kashe Sayyadina Zubairu (RA) ranar Alhamis 20 ga Jimada Ula, shekara ta 36 Bayan Hijira, yana da shekera 67.

7. Abdurramani bin Auf

“Allah Ya yi maka albarka cikin abin da ka bayar Ya kuma sanya albarka cikin abin da ka bari.” – Manzon Allah (SAW) ga Abdurraham dan Auf

Sunnansa Abdulrahaman dan Auf dan Abdul-Haris dan Zuhura dan Kilabu dan Murra dan Ka’ab dan Lu’ayyi. A lokacin Jahiliyya ana kiransa “Abdul Amru,” yayin da ya musulunta sai Manzon Allah (SAW) ya kira shi Abdurrahaman.

Shi ne dayan mutum takwas da suka fara musulunta. Daya daga cikin sahabbai goma da aka yi wa bushara da gidan Aljanna. Daya daga cikin ma’abota shawara shida da Sayyadina Umar  (RA) ya nada, don zaben halifa a tsakaninsu. Daya daga cikin mutanen da ke ba da fatawa a Madina alhalin Manzon Allah (SAW) yana raye saboda yarda da shi da ya yi, sannan yana daya daga cikin sahabban Annabi (SAW) da Allah Ya wadata su da dukiya mai yawa kuma suke ciyar da ita wajen daukaka addinin Allah.

Ya musulunta bayan musuluntar Sayyadina Abubakar (RA) da kwana biyu. Yana daga Musulmin farko da suka sha bakar azaba daga kafiran Makka amma suka yi hakuri suka tabbata bisa imaninsu, suka gaskata Allah da ManzonSa (SAW), har ta kai su ga yin kaura zuwa kasar Habasha. Kuma cikin rukunin farko na Musulmin da suka yi kaura zuwa Madina. Manzon Allah (SAW) ya hada shi ’yan uwantaka shi da Sa’adu dan Rabi’u, mutumin Madina.

Ya yi dauki-ba-dadi da kafirai a Yakin Badar har sai da ya kashe makiya Allah. A Yakin Uhudu kuwa Sayyidina Abdurrahaman bin Auf (RA) yana cikin tsirarin sahabbai da suka tabbata kan duga-dugansu, suka kame suka sandare don kare Manzon Allah (SAW) sai da aka yi masa munanan raunuka 21 a wannan yaki.

Irin wannan yaki na Sayyadina Abdurrahaman (RA) kadan ne, idan aka kwantanta da wanda ya yi da dukiyarsa. Akwai wani lokaci da Manzon Allah (SAW) ya yi nufin aika masu jihadi, sa ya ce: “Ku yi sadaka domin ina so zan ttura mayaka.” Nan da nan Abdurrahaman (RA) ya je gidansa ya dawo da sauri ya ce: “Ya Ma’aikin Allah ina da (Zinare da Dirhami) dubu hudu. Na ranta wa Ubangijina 2000 na bar wa iyalina 2000.” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce da shi “Allah Ya sanya maka albarka cikin abin da ka bayar, Ya kuma sanya albarka cikin abin da ka bari.”

Yayin da Manzon Allah (SAW) zai fita Yakin Tabuka, ya umarci sahabbai su kawo gudunmawa, Sayyadina Abdurahaman (bayan kasancewarsa cikin mayaka) yana cikin sahun farko wajen kawo gudunmawa, inda ya bayar da mudun zinare 200. Manzon Allah (SAW) ya ce da shi: “Shin ka bar wa iyalanka wani abu kuwa?” Sai ya ce: “Eh, na bar musu abin da Allah da ManzonSa suka yi alkawari na arziki da alheri a Lahira.”

Bayan wafatin Manzon Allah (saw), Sayyadina Abdurrahman ne ya rika daukar nauyin iyayen muminai, (matan Annabi SAW) yana daukar nauyin tafiye-tafiyensu, yana tafiya Hajji tare da su, yana kula da dukan bukatunsu. Wannan wani matsayi ne da Sayyadina Abdurrahman ya kebantu da shi da kuma amincewa da su iyayen muminai suka yi da shi. Akwai wata gonarsa da ya sayar Zinare dubu 40 ya raba kudin tsakanin Banu Zuhuratu (dangin mahaifiyar Annabi (SAW) da matan Annabi (SAW) da talakawa Musulmi. Yayin da aka kai wa Nana A’isha (RA) nata kason, ta ce: “Wane ne ya aiko da wannan dukiya?” Aka ce: “Abdurrahaman bin Auf ne.” Sai ta ce: Manzon Allah (SAW) ya ce (da mu): “Babu wanda zai tausaya gare ku bayana, sai masu hakuri.”

Akwai wata rana da wani ayarin fatauci na Sayyadina Abdurrahaman, kunshe da rakuma 700, dauke da abinci da sauran kayan bukatu ya iso. Ayarin na shigowa Madina, sai garin ya rude da sowa da murna. Nana A’isha (RA) ta ce: “Hayaniyar me nake ji haka? Aka ce: “Ayarin Abdurrahman bin Auf ne ya iso, na rakuma 700, dauke da kayan abinci.” Sai ta ce: “Allah Ya sanya masa albarka cikin abin da ya bayar a duniya, ladan Lahira kuwa, shi ne ya fi girma. Hakika, na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Abdurrhman dan Auf, zai shiga Aljanna yana mai jan-ciki.”

Kafin rakuman nan su durkusa, mai bushara ya kai masa labarin abin da Nana Ai’sha (RA) ta fada. Nan da nan, ya ruga gare ta, ya ce: “Ya Umma! Haka kika ji haka daga Manzon Allah (SAW)?”  Ta ce: “Eh” Ai sai farin ciki ya kama shi ya ce: “Idan har na samu iko, to, sai na shige ta (Aljanna) ina tafe. Ki shaida ya Umma! Wannan ayari da duk abin da suke dauke da shi, kayan abinci da na bukatu na bayar da su, saboda Allah. A lokacin kuma ya yi sadakar dirhami dubu 40 na azurfa.

Tun daga wannan babbar rana da aka yi masu bushara da shiga Aljanna sai ya kara kaimi wajen ciyar da dukiya ba-ji-ba-gani. Akwai ranar da ya yi sadaka da mudu 200 na zinare. Sannan ya bai wa masu tafiya jihadi dawaki 500, ya kuma bai wa wadansu rakuma 1500.

A cikin rashin lafiya da ya yi wafati, ya ’yanta bayi da yawa. Ya yi wasiyyar a kai wa ragowar wadanda suka halarci Yakin Badar zinare 400 kowannensu. A wannan lokacin su 100 ne (Zinare dubu 40 ke nan). Kuma ya yi wasiyyar a bai wa kowace daga cikin matan Annabi (SAW) dukiya mai yawa. Sau d a yawa Nana Ai’sha (RA) kan yi masa addu’a ta ce: “Allah Ya shayar da shi ruwan Salsabilu, (a Aljanna yake).”

Bayan duk wannan sai da ya bar wa magadansa dukiya mai dimbin yawa: Ya bar musu rakuma dubu da dawaki 100 da awaki dubu uku. Kowace daga matansa kuma ta samu zinare dubu 80 sauran zinare da azurfa kuwa da masaki aka rika raba su ga sauran magadansa. Duk wannan, albarkacin addu’ar da Manzon Allah (SAW)  ya yi masa ne, da ya ce, “Allah Ya sanya maka albarka cikin abin da ka bari.”

Sayyadin Abdurrahman (RA), ya rasu a shekara ta 32 Bayan Hijira, yana da shekara 75. An binne shi a Baki’a ya bar ’ya’ya 36: maza 28, mata 8. Sayyadina Usman (RA) ne ya yi masa Sallah, bisa wasiyyar da ya yi a kan haka. Cikin manyan sahabban da suka kai shi kabari har da kawun Manzon Allah (SAW), Sa’adu dan Abu Wakkas da Sayyadina Aliyu dan Abu Dalib (Allah Ya kara musu yarda).

Imam Ahmad Adam Kutubi,

Nigeria Police Force,

Zone 7, Police Headkuarter,

Abuja. 08036095723