Sahabbai Goma ’yan Aljannah (6)

8.  Sa’adu bin Abu Wakkas “Harba ya Sa’adu, harba! Mahaifana fansa ne gare ka.” – Manzon Allah SAW). Shi ne Sa’adu dan Abu Wakkas Bazuhure (daga Banu Zuhrata). Dangin Aminatu, Mahaifiyar Manzon Allah (SAW). Daya daga cikin mutum uku da suka fara shiga addinin Musulunci, kuma daya daga cikin sahabbai goma da aka yi wa […]

Sahabbai Goma ’yan Aljannah (6)
Sahabbai Goma ’yan Aljannah (6)

8.  Sa’adu bin Abu Wakkas

“Harba ya Sa’adu, harba! Mahaifana fansa ne gare ka.” – Manzon Allah SAW).

Shi ne Sa’adu dan Abu Wakkas Bazuhure (daga Banu Zuhrata). Dangin Aminatu, Mahaifiyar Manzon Allah (SAW). Daya daga cikin mutum uku da suka fara shiga addinin Musulunci, kuma daya daga cikin sahabbai goma da aka yi wa bushara da gidan Aljanna.

 

Shigarsa Musulunci:

Sayyidina Sa’ad bai yi wata wata ba, ya amsa kira Allah, har ya zamo cikin mutum uku ko hudu na farko da suka karbi addinin Musulunci. Manzon Allah (SAW) ya yi matukar farin ciki da musuluntarsa, saboda alamun jarunta da ya gani daga gare shi.

Yayin da mahaifiyarsa Hannatu bint Sufyan, ta ji labarin ya shiga addinin Musulunci, sai ranta ya baci matuka, har ma ta ce, idan bai fita daga Musulunci ba, to za ta shiga yajin cin abinci da shan ruwa har ta mutu (don hakan ya zame masa abin gori). Amma bai bar Musulunci ba. Ita kuma ta kaurace wa abinci da ruwa duk ta bi ta bushe, ta kanjame, ta jeme! Sayyidina Sa’ad (RA), ya yi rarrashin duniyar nan, amma ta dage kan sai dai ta mutu da yunwa da kishirwa. Da ya ga haka sai ya ce: “Ya mahaifiyata! Duk da tsananin kaunata gare ki, wallahi, Allah da

ManzonSa (SAW), su ne mafiya soyuwa a gare ni. Kuma wallahi, idan rai dari ke gare ki, a ce su rika fita daya bayan daya, har ki mutu, ba abin da zai sa in bar wannan addinin nawa (Musulunci). Ai da ta ga shi ma da gaske yake yi, sai ta ba da kai! Ta koma cin abinci kamar da, kan wannan ne, Allah Ya saukar da fadinSa:

“Idan (mahaifanka) suka tsananta (tilasta) maka a kan ka tara wani da ni (wajen bauta ko ki bin umarniNa) bisa abin da ba ka da sani game da shi, to kada ka yi musu biyayya. Ka zauna da su a cikin duniya gwargwadon shari’a (kana mai kyautata musu), amma ka bi tafarkin wanda ya mayar da lamari zuwa gare Ni. Makomarku zuwa gare Ni take, sannan in ba ku labari game da abin da kuka zamo kuna aikatawa.”  (Lukman:15)

A lokacin Yakin Badar, Sayyidina Sa’adu (RA), shi da kanensa Umairu (RA) sun yi jihadi sosai, har kanensa Umairu ya yi shahada. A Yakin Uhudu kuwa, Sa’ad (RA) yana cikin tsirarin sahabban da suka tsaya tare da Manzon Allah (SAW), yayin da kafirai suka watsa rundunar Musulmi. A lokacin idan Sayyidina Sa’ad ya dana bakarsa, duk kibiyar da ya harba sai ta kashe kafiri. Manzon Allah (SAW) yana kara masa kaimi da cewa: “Harba Sa’ad, harba! Mahaifana fansa ne gare ka!”

Sayyidina Sa’ad (RA) ya zamo yana alfahari da wannan magana ta Annabi (SAW) gare shi. Yakan ce, “Babu wanda Manzon Allah (SAW) ya hada sunsansa da na mahaifansa sai ni!”

Jarumtar Sayyidina Sa’adu (RA) ta dada fitowa fili, yayin da Halifa Umar (RA) ya yi nufin yaki da kasar Farisa (Iran), inda ya hada babbar runduna kunshe da manyan mayaka daga kowace kasa da ke karkashin daular Musulunci a lokacin. Sai ya tambayi manyan mashawartansa, kan wanda zai nada, ya shugabanci wannan babbar runduna ta yaki. Gaba dayansu, sai suka ce: “Ai wannan aiki sai Sa’ad dan Abu Wakkas!” Nan da nan ya kira shi, ya ba shi tutar yaki, ya yi masa  ban-kwana tare da wasiyyoyi, ya ja rundunar zuwa kasar Farisa.

Wannan babban yaki a tsakanin Musulmi da Farisawa shi ake kira “YAKIN KADISIYYA,” wanda Musulmi suka fatattaka gayyar Farisawa, har aka kshe jagoran yakinsu “RUS TUM,” aka soke kansa a kan tsinin mashi. Har sai da ta kai Musulmi kan kira Bafarise ya karbi makaminsa ya kashe shi da shi! Wadanda suka fada ruwa suka mutu (daga Farisawa kuwa) sun kai kimanin mutum dubu 30. Ganima kuwa, duk yadda ka shata ka fada ba ka iyawa ba. Wannan wani babban budi ne daga Allah ga daular Musulunci a karkashin jagorancin Sayyidina Sa’adu (RA).

Sayyidina Sa’ad (RA) ya yi tsawon rai yana kuma daga cikin wadanda Allah Ya wadata da dukiya. Yayin da mutuwa ta kusato masa sai ya sa aka dauko masa wata rududdugaggiyar jabba (riga) tasa ta gashi, ya ce: “Ku yi mini likkafa ni da ita. Domin da ita na halarci Yakin Badar. Don haka, nake so, in sadu da Ubangiji da ita.” An binne shi a makabartar Baki’a. (Allah Ya kara masa yarda).

 

9.  Sa’idu bin Zaidu (Allah Ya kara masa yarda):

“Ya Ubangiji tunda ba Ka nufe ni da saduwa da wannan alheri ba, (Musulunci) to, kada Ka hana wa dana Sa’idu.” – Zaidu dan Amru

 

Shi ne Sa’idu dan Zaidu dan Amru dan Nufailu dan Abdul Uzza dan Ribahu dan Kurdu dan Rizahu dan Addi dan Ka’abu dan Lu’ayyu dan Galibu, Bakuraishe, Ba’adawe. Daya daga cikin Musulmin farko, kuma daya daga cikin sahabbai goma da aka yi wa bushara da gidan Aljanna.

Mahaifinsa Zaidu dan Amru ya kasance mai kyamar miyagun al’adun mutanen Makka da bautarsu ga gumaka a lokacin Jahiliyya. Sakamakon haka ya bar Makka, shi da Warakatu dan Naufal, (Baffan Nana Khadija) zuwa wasu kasashe, don neman addinin kwarai. Bahahife na Annabi Ibrahim (AS) shi Warakatu sai ya rungumi Nasaranci, amma shi Zaidu, sai ya ki amincewa da shi. Daga karshe, sai ya hadu da wani babban malamin Nasara, wanda ya ba shi shawarar ya koma Makka, a can, Allah zai aiko Annabin karshe, ya yi masa wasiyya da ya bi shi.

Zaidu dan Amru (RA) ya koma Makka ya yi ta sauraron aiko Annabi, (SAW) har tsufa ta cin masa. Da ya ga alamar ba zai samu ganin lokacin ba, sai ya yi wa amininsa, Amiru dan Rabi’atu wasiyya da in wannan Annabi ya bayyana ya isar da sallamarsa gare shi. Ya ce: “Domin na yi imani da shi, na gaskata abin da ya zo da shi.” Kafin ransa ya fita, sai ya daga kansa sama ya ce: “Ya Ubangiji! Tunda ba ka nufe ni da saduwa da wannan alheri ba, (addinin Musulunci) to, kada Ka hana wa dana Sa’idu.”

A karkashin kulawar wannan nagartaccen uba, Sayyidina Sa’idu (RA) ya taso. Da kuma irin akidarsa (ta tauhidi) ya tarbiyyantu. Sakamakon haka, Ubangiji Yana aiko Manzon Allah (SAW), sai Sayyidina Sa’idu (RA) ya amsa, ya shiga addinin Musulunci, tare da matarsa Fadimatu ’yar Khaddabi, kanwar Sayyindina Umar RA.

A lokacin bai wuce shekara ashirin a duniya ba. Ya hadu da azaba iri-iri daga kafiran Makka, tare da sauran Musulmin Farko.  Duk da haka, shi da matarsa, suna cikin wadanda suka zama sanadin musuluntar Sayyidina Umar (RA), shi ne ma ya jagorance shi, zuwa wurin Manzon Allah (SAW) a gidan Arkam bin Abu Arkam.

Imam Ahmad Adam Kutubi,

Nigeria Police Force, Zone 7, Police Headkuarter, Abuja. 08036095723