Sahun Buhari na bi wajen rage cunkoso a gidan Yari-Hassan Zarma

Minista a ma’aikatan ayyuka, gidaje  da makamashi Alhaji Suleiman Hassan Zarma, ya ce ya bi sahun shugaban kasa Muhammadu Buhari ne wajen rage cunkoso a gidan Yari. Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya biya tara da diyar wasu fursunoni 36 da aka sake su a babban gidan Yari na jihar  Gombe. Ya […]

Sahun Buhari na bi wajen rage cunkoso a gidan Yari-Hassan Zarma

Minista a ma’aikatan ayyuka, gidaje  da makamashi Alhaji Suleiman Hassan Zarma, ya ce ya bi sahun shugaban kasa Muhammadu Buhari ne wajen rage cunkoso a gidan Yari.

Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya biya tara da diyar wasu fursunoni 36 da aka sake su a babban gidan Yari na jihar  Gombe.

Ya kuma yi amfani da wannan dama ya ja kunnen fursunonin a gaban gidan yarin gabannin a sake su inda yace yana tsammanin wannan rana za ta kasance ranar farin ciki a gare su domin wasun su sun shiga gidan ne bisa aikata kananan laifuffuka wasu kuma bisa kuskure.

Suleiman Zarma, ya kara cewa dukkan su matasa ne da ake bukatar gudumawa su a tsakanin al’umma dan haka su daure su zama mutane na gari.

Ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da daidaikum mutane da kungiyoyi cewa suma su shigo su cire wasu dan a rage cunkuson a gidajen yarin.

Wannan sai ya godewa Allah na yadda ya ba shi dama ya iya biyan tarar fursunonin aka yanta su.

Daga nan sai ya ce idan ba’a zuwa ana rage su gidan zai cika da yawa domin yanzu haka ma gidan ya kamata ya dauki mutane 400 ne amma saboda cunkoso mutane fiye da 1000 ne a gidan.

Da suke godiya a madadin wadanda aka biyawa tarar Dauda Adamu da Daniel Ambrose, godewa Allah suka yi na yadda ya bai wa Ministan dama ya cire su a wannan gidan inda suka ce sun koyi darasi na zama a gidan.

Kamar shi Dauda Adamu, cewa ya yi da ko sallah bai cika yi ba amma yanzu dan zaman da ya yi a gidan kason yasa sallah ba ta wuce shi.